Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Rajin Shugabanci Sun Fara Muhawara Akan Matsayin Tattalin Arzikin Jihar Jigawa


Sabon Gwamnan Jigawa
Sabon Gwamnan Jigawa

Mako guda bayan kaddamar da majalisar zartarwa a jihar Jigawa ta Najeriya, al’ummar jihar na ci gaba da dakon ji daga gwamnan jihar Malam Umar Namdi game da halin da lalitar jihar ke ciki.

JIGAWA, NIGERIA - Yanzu haka dai ‘yan siyasa da kwararru akan harkokin kudade da sha’anin tattalin arziki da kuma kungiyoyin rajin shugabanci na gari sun fara mahawara dangane da batun.

Kamar galibin jihohin Najeriya, yanzu dai an shiga wata na uku kenan da kafa sabuwar gwamnati a jihar Jigawa, bayan da sabon gwamnan jihar Malam Umar Namadi ya karbi ragamar mulki a ranar 29 ga watan Mayun bana.

Koda yake gwamna Namadi ya yi amfani da wannan rana wajen bayyana kudirorin gwamnatinsa guda 12 ga ‘yan Jigawa da zasu kasance alkibilar gwamnatin zuwa shekaru hudu masu zuwa, amma har ya zuwa yanzu bai fayyace yanayin da ya samu lalitar Jigawa ba, al’amarin da ya haifar da mahawara a tsakanin ‘yan siyasar Jihar da masana da kuma kungiyoyi masu rajin shugabanci na gari.

A hirar shi da Muryar Amurka, Nasiru Garba Dantiye, tsohon dan Majalisar Tarayya kuma jigo a Jam’iyyar hamayya ta PDP a jihar Jigawa ya bayyana cewa, “Wannan Magana ce ta hakki, ba magana ce ta Jam’iyya ba, ‘yan Jihar Jigawa hakkin su ne su san halin da jihar su ke ciki, menene dalilin da ya sa ake wannan rufa-rufar? Akwai wani abu ne da aka yi ba’a so mu ‘yan jihar Jigawa mu sani? A dokar Najeriya babu damar a boye mana abin daya shafe mu”.

Kungiyar kwamishinoni 18 da Gwamna Namadi ya nada domin taya shi aiki, wani lamarin da ya ja hankalin al’ummar jihar, musamman ‘yan siyasa, la’akari da cewa, galibin su tsoffin kwamishinonin gwamnatin baya ne.

Sai dai Comrade Salisu Mazge Gumel jigo a kungiyoyin ci gaban al’umma a jihar ya ce su ‘yan Jigawa ba su da matsala saboda kwamishinan tsohuwar gwamnati ya dawo, tunda duka Jam’iyya daya ce, amma suna da bukatar sanin halin da asusun gwamnatin su ke ciki.

Dangane da ko dokar kasa ce ta bukaci halin da shugaba kamar Gwamnan jiha ya samu lalitar gwamnati, Dr Sanusi Garba shugaban sashen nazarin al’amuran kudade da gididdiga a Jami’ar Tarayya dake Dutse ya ce, “Gaskiya doka ce domin akwai sharudan doka da suka shata cewa, duk wani shugaba idan ya zo zai karbi daftarin mulki daga tsohon shugaba kuma a cikin wannan daftari shine bayani na kadarori da basussuka da suke kan gwamnati”.

Masu kula da lamura dai na Gavin cewa, kasancewar gwamna Umar Namadi masani kuma kwararre a fannin hada-hadar sarrafa kudade, babu ko shakka ba zai rasa masaniya ba akan abin da kwararrun ke ambatawa, sai dai a iya cewa, yana da dalilan sa na yin shiru game da batun, illa dai kawai bai kai ga sanar da ‘yan Jigawa dalilan nasa ba.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Kungiyoyin Rajin Shugabanci Sun Fara Muhawara Akan Halin Dukiyar Jihar Jigawa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG