KANO, NIGERIA - Da alama dubban daliban dake karatu a Jami’o’in Gwamnatin tarayya a Najeriya na fuskantar barazanar fita daga makaranta ba tare da sun kammala karatun ba biyo bayan karin kudin makaranta da ya gagari galibinsu biya.
A karkashin sabon tsari kusan Naira dubu dari uku kowane dalibi zai biya kudin karatu na shekara wanda a baya ake biyan kudi kasa da Naira dubu hamsin.
Wannan batu na karin kudin karatu na daya daga abubuwan da suka haifar da takaddama tsakanin Gwamnati da malaman jami’o’in Gwamnatin tarayya, inda malaman suka kwashe watanni takwas suna taka yajin aiki, al’amarin da ya kai su ga gurfana a gaban kotu.
Ya yin da wa’adin biyan kudin makaranta ke cika a ranar Alhamis din nan, rahotanni na nuni da cewa, adadi mai yawa na daliban Jami’ar ta Bayero ba su kai ga biyan kudin makarantar ba, al’amarin da ke barazana ga makomar karatun na su.
Malam Sadi Salisu wani daga cikin iyayen daliban dake karatu a jami’o’i mallakar Gwamnatin tarayya ya roki Gwamnatin da ta yi gaggawar cire karin kudin, musamman la’akari da halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ‘yan kasa ke ciki.
Yayin da wa’adin rufe rijistar dalibai na bana a Jami’ar Bayero Kano ke cika, kungiyar tsoffin daliban Jami’ar lokacin tana karkashin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, ta shiga tsakani.
Dr. Goni Umar Faruk shugaban kungiyar na kasa. Ya ce ”hankalin mu ya tashi sosai lokacin da muka sami labarin cewa, daliban da dama a Jami’ar Bayero ba za su iya ci gaba da karatun su ba saboda karin kudi da aka yi daga dubu talatin zuwa dubu dari biyu da sittin, iyaye da yawa wancan ma ba sa iya biya ballantana yanzu.”
Baya ga kara wa’adin kungiyar tsaffin daliban Jami’ar Bayeron na muradin mahukuntan jami’ar da su amince da tsarin biya na daki-daki domin iyaye su samu sukunin biya, saboda rashin baiwa daliban dama su ci gaba da karatu babbar barazana ce, domin kuwa aikace-aikacen miyagun ayyuka na iya karuwa a cikin al’umma.
Kimanin wata guda da dawowa sabon zangon karatu, amma a galibin Jami’o’in Najeriya cikin su kuwa har da Jami’ar ta Bayero a Kano, sai dai da yawa daga cikin daliban har yanzu ba suyi rijista ba.
Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim kwari:
Dandalin Mu Tattauna