Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KANO: An Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Harkokin Bunkasa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu


Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Harkokin Bunkasa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu
Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Harkokin Bunkasa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu

Taron masu ruwa da tsaki kan harkokin bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu ya koka kan yadda mutanen lardin arewacin Najeriya ba sa samun damar cin gajiyar lamani da tallafin da gwamnatin tarayya, bankuna, cibiyoyin raya tattalin arziki kan bayar da nufin ciyar da tattalin arzikin al’uma gaba.

Mahalarta taron wanda ya wakana a tsangayar nazarin harkokin kasuwanci da tattalin arziki, wato Dangote Business School da ke Jami’ar Bayero a Kano, sun mayar da hankalin kan koma bayan da masu kananan sana’o’i da matsakaitan masana’antu a jihohin arewa ke fuskanta saboda rashin hanyoyin tallafi da lamanin kudade daga cibiyoyin hada hadar kudade na gwamnati da masu zaman kansu, al’amarin da ke haifar da karancin ayyukan yi da koma bayan tattalin arziki a yankin arewacin Najeriya.

Alhaji Shehu Dalhatu, daya daga cikin masu shirya taron, yace damarmakin da ya kamata mutane musamman mata da matasa masu kananan masana’antu su ci gajiyarsu ba sa samu, saboda ba su san hanyar da za su bi ba.

Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Harkokin Bunkasa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu
Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Harkokin Bunkasa Kanana Da Matsakaitan Masana’antu

An dade ana barin ‘yan arewa a baya wajen cin gajiyar tsare tsaren tallafa wa masu kananan sana’o’i da matsakaitan masana’antu da gwamnatin tarayya kan bullo dasu. Na baya bayan nan shi ne lamani ko rancen kudade da gwamnatin Najeriya ta fitar na biliyoyin naira ta hannun bankin bunkasa tattalin arzikin kasa wato Nigerian Development Bank, inda aka ce fiye da kashi 40 na kudaden sun tafi jihar Lagos.

Malam Salihu Idris, da ke zaman manajan ayyuka na musamman a bankin, na daga cikin mahalarta wannan taro, yace rashin ganewa ya sanya galibin masu kananan masana’antu da ‘yan kasuwa ba sa bin ka’idojin tafiyar da kasuwanci na zamani, ba sa yin rijista da hukumomin gwamnati, kuma ba kasafai suke kiyaye sharrudan da bankuna kan shimfida ba kafin samun kudaden lamani ko bashi.

Da alama masu kananan masana’antun sun karbi wannan kalubale.

Hajiya Hussaina Ahmad Umar na da karamin kamfanin matsar gyada a rukunin kananan masana’antu a unguwar Dakata da ke Kano, ta ce sun yi damara, sun shirya dukkanin sharrudan da ake bukata a cika kuma zasu yi kokarin cikawa, sannan za su je bankunan kasuwanci domin cike takardun da suka kamata.

To sai dai daya daga cikin masu gabatar da Makala a yayin taron Farfesa Murtala Sabo Sagagi, ya ce akwai kalubale.

“Tilas ne sai an hada karfi da karfe, lallai ne sai gwamnatocin jihohi sun shiga tsakani, don duk abin da aka ce an yi shi a Abuja, muddin jihar ka ba ta rungume shi ba, to mutanen jihar ba zasu ci gajiyar sa ba.”

Ko da yake taron ya kunshi dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren tafiyar da harkokin masu kanana da matsakaitan masana’antu a Kano, amma gwamnatin jihar Kano ba ta sami sukunin tura ko da guda daga cikin jami’anta ba, duk kuwa da goron gayyata da masu shirya taron suka ce sun tura wa gwamnatin.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG