Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masharanta Sun Fara Mayar Da Martani Dangane Da Nasara Ko Tasirin Zanga Zangar NLC


Zanga-zangar NLC a Abuja, Najeriya
Zanga-zangar NLC a Abuja, Najeriya

Biyo bayan zanga zangar lumana na rashin jin dadi game da halin kunci da al’umar kasar suka shiga, masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun fara mayar da martani dangane da nasara ko tasirin zanga zanga.

Kasa da sa’o’i 24 ne kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta gudanar da zanga zangar lumana domin bayyana rashin jin dadi game da halin kunci da al’umar kasar suka shiga biyo bayan tashin farashin kayayyaki a kasar sanadiyyar janye tallafin gwamnati a albarkatun mai na kasar.

Yadda aka gudanar da zanga-zangar lumana ta NLC a Najeriya
Yadda aka gudanar da zanga-zangar lumana ta NLC a Najeriya

Tashin farashin kayayyaki da faduwar darajar naira, karin kudin makaranta, musamman makarantun ilimi mai zurfi da kuma tsadar sufuri na daga cikin batutuwan dake damun ‘yan Najeriya kuma sune kungiyoyin ma’aikata na kasar karkashin uwar kungiyar kwadago ta NLC ken una adawa da su har-ma ta gudanar da zanga zangar lumana.

Duk da cewa, an gudanar da zanga zangar ne a jihohin kasar 36 da kuma babban birnin kasar Abuja, wasu daga cikin manazarta akan harkokin kwadago na cewa, kwalliya ba ta kai ga biyan kudin sabulu ba.

Zanga-zangar Lumana Ta Kungiyar NLC a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00

A hirar shi da Muryar Amurka, Dr Mansur Datti malami dake koyar da ilimi harkokin kwadago da nagartar aiki a kwalejin nazarin harkokin gudanarwa da sha’anin Mulki ta Kano yace

Bayan taruka da masu ruwa da tsaki da kyar aka rinjayi kungiyar kwadago ta gudanar da wannan zanga zanga kana daga bisani ta tafi yajin aiki na gama gari, saboda tasirin yajin aiki wajen kassara ayyukan gwamnati, amma duk da haka NLC ta nuna kamar ba da gaske take bai”

To amma a cewar, Comrade Sa’idu Bello, tsohon mamba a kwamitin koli na kungiyar kwadago ta Najeriya, zanga zangar lumanar ta NLC tayi armashi.

Gaskiyar lamari wannan fitowar da aka yi an samu nasara, tunda a baya ba’a samu irin wannan nasara ba, saboda NLC ta kira-ta-kira amma babu wanda yace kala, ‘yan kasa suka watsawa kungiyar kwadago kasa a ido, shine ya sanya a baya suka kasa yin komai.”

Sai dai duk da haka gwamnati da kungiyar kwadago nada damar fitar da talakawan Najeriya daga wannan yanayi na tsadar rayuwa, a cewar Dr Mansur Datti.

Baban fatan ‘yan Najeriya dai shine bangarorin biyu su fahimci juna ta yadda zasu cimma yarjejeniyar da zata haifar da samun sauki ga yanayin da aka tsinci kai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG