Zanga-zangar lumana ta neman a yi garambawul a ayyuakan ‘yan sandan Najeriya da ta rikide ta zama tarzoma, yanzu ta zama wata dama ga wasu matasa a wasu sassa na Najeriya ta kai farmaki ga rumbunan adana kayan abinci na gwamnati da nufin kwasar ganima.
Rahotanni sun tabbatar da wakanar farmaki a jihohin Filato, Taraba, Kaduna, Lagos, Osun, Cross River da Kwara da sauran su, inda matasan suka yi amfani da karfin tuwo wajen bude rumbunan da gwamnati ke ajiye kayayyakin abinci da aka ce an tanade su ne domin tallafa wa jama’a saboda annobar coronavirus a watannin baya.
Alhaji Mohammed Sabo Nanono, Ministan ma'aikatar noma da raya karkara ta Najeriya, ya yi tsokaci game da musabbabin wannan matsala, kuma ya ce a shirye gwamnati ta ke ta taimaka wa manoma a fannin noman rani da basu irin hatsi da zasu shuka kama daga masara, shinkafa, dankali da wake.
Yanzu haka dai gwamnatin Kano ta kafa kwamitocin tsaro a matakan kanananan hukumomi da shiyyoyi domin tabbatar da zaman lafiya, kamar yadda kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo ya bayyana.
Kwamishinan ya kara da cewa jihar Kano jihar kasuwanci ce, don haka al'ummar jihar su guji tada zaune tsaye, ya kuma ce gwamnatin jihar ta kafa kwamitoci don wayar da kan jama'a kan muhimmancin zaman lafiya.
Su ma dattawan Arewa suna kara yin kira ga jama'a da gwamnatoci akan su himmatu wajen ganin an samar da shugabanci na adalci da tabbatar da zaman lafiya a cikin al'umma.
Ga cikakken rahoton cikin sauti.
Facebook Forum