Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 10 a gidan gyaran hali ga wani dan shekaru 15 saboda samun shi da laifin furta laffuzan da kotun ta ce sun saba wa shari’ar musulinci.
A cikin watan Maris na wannan shekarar ta 2020 ne wani matashi mai suna Shariff Yahaya Aminu da ke unguwar Sharifai a cikin birnin Kano ya wallafa wani rubutu a shafin Facebook da kuma rera wata waka mai kunshe da kalaman da shari’ar musulinci ta haramta a alakanta su da mahallici Allah ta’ala da mazon sa.
Shi kuwa dayan matashin mai suna Umar Faruk Bashir da iyayen sa ke zaune a unguwar Sharada an tuhume shi da aikata makamantan wadancan laffuza ne a yayin da musu ya kaure tsakanin sa da wasu.
Bayan amsa laifukan da ake tuhumar su alkalin babbar kotun shari’ar Musulincin Kadi Aliyu Muhammad Kani, ya ce kotu ta yi la’akari da litattafan mazahabar malikiyya ne wajen yanke hukunci da ya dace da matasan biyu.
Baba Jibo Ibrahim, da ke zaman kakakin kotunan jihar Kano ya yi Karin haske akan hukuncin inda ya ce an yanke wa daya daga cikin matasan hukuncin zaman gidan gyaran tarbiya na tsawon shekara 10 da kuma aiki mai tsanani, na biyun kuma da ya danganta manzon Allah (S.A.W) da shirka, kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a karkashin doka mai lamba 382 ta kotun shari’a. Ko da ya ke, kotun ta basu dama su daukaka kara nan da kwana 30.
Barista Abdul Adamu Fagge tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Kano, ya ce kundin tsarin Mulkin Najeriya ya ba kotun shari’a damar daukaka kara akan abubuwan da suka shafi rabon gado, rabon rike yara da sauran abubuwan neman hakki, amma idan batun laifi ne, dole ne a daukaka kara a kotun jiha. Ya kuma ce tunda kotun shari’a ce ta yanke hukuncin, matasan na da dama su daukaka kara a babbar kotun jiha.
Haka zalika, Barista Abdul Adamu Fagge ya fayyace wanda doka ta rataya wa alhakin tabbatar da wannan hukunci bayan kammala shari’a. Ya na mai cewa gwamnatin jiha ce ke da hakkin aiwatar da hukunci duk da cewa kotun shari’a ta yanke hukunci.
Shariff Yahaya Aminu, ba shi ne mutum na farko da kotun shari'ar Musulci ta jihar Kano ta yankewa hukumcin kisa dangane da aikata irin wannan laifin ba, tun bayan da jihohi da dama a arewacin Najeriya suka kafa kotunan shari’ar Musulunci a farkon shekara ta dubu biyu.
A shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, kotun ta yankewa wadansu mutane tara da suka hada da mace guda hukumcin kisa wadanda kotun ta same su da laifin a karkashi doka ta 404 na kundun tsarin dokokin shari'ar musulunci ta shekara 2000 ta jihar Kano.
Kotun shari'ar musuluncin ta jihar Kano ta kuma yankewa wani malamin addinin musulunci mai suna Abdul-Aziz Dauda da aka fi sani da Abdul inyas, hukumcin kisa ta hanyar taraya a watan janairun shekara ta dubu biyu da goma sha shida, bayan ta same shi da laifin furta kalaman batanci ga manzon Allah.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari
Facebook Forum