Hukumomin jihar ta Kano ne suka bada umarnin sake bude makarantun bisa shawarar kwamitin yaki da cutar Corona na tarayya tare da alkawarin kiyaye dokoki da ka’idojin da kwamitin ya shimfida, kamar aikin feshin kashe kwayoyin cutuka a harabar makarantu da samar da kyallen rufe hanci da baki ga dalibai da malamai da kuma sinadaran wanke hannu.
Dr. Kabiru Ibrahim Getso dake zaman kwamishinan muhalli na Kano ya ce sun gudanar da aikin feshin kashe kwayoyin cutuka a makarantun kafin kaiwa ga wannan gaba. Ya ce sun gudanar da aikin feshin ne a makarantun gwamnati da na masu zaman kansu.
Domin tabbatar da tazara a tsakanin dalibai a ajujuwa, akwai wasu matakai da aka dauka da suka hada da ware ranaku ga daliban aji daya da na biyu da rarraba yaran a cikin sauran ajujuwan, haka zalika ‘yan ajujuwan uku da hudu da biyar suke da ranakun karatu domin tabbatar da ganin ba a cusa daliban wuri guda ba.
Yanzu haka dai iyaye na tsokaci game da wannan yunkuri na sake bude makarantu a Kano bayan kasancewar a kulle tsawon watanni bakwai.
A nata bangaren, ma’aikatar kula da harkokin ilimin gaba da sakandare tace nan gaba kadan zata bude makarantun dake karkashin kulawar ta.
Ga dai rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:
Facebook Forum