A saboda haka majalisar dokokin jihar ta umarci bangaren zartarwa na gwamnati ya gaggauta daukar malamai dubu 15 domin cike gibin da ake da shi.
A cikin wani rahota da kwamitin majalisar wanda ya yi nazarin halin da lamuran ilimi ke ciki a Kano, ya alakanta yadda dalibai ke faduwa jarabawa a matakai dabam-daban da rashin wadatattu da kuma kwararrun malamai a makarantun.
Hakan dai na zuwa ne kimanin shekara guda bayan da gwamnatin jihar Kano ta ayyana tsarin ilimi dole kuma kyauta a matakin firamare zuwa sakandare ga ‘ya’yan jihar.
Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar Honarabul Kabiru Hassan Dashi, ya bayyana wa Muryar Amurka cewa akwai rashin malamai matuka a makarantu, kuma hakan shi ya ke kara kawo koma baya a harkokin ilimi a jihar, a dalilin haka ne kwamitin ya bai wa gwamnatin jihar shawarar daukar malamai a jihar.
Mai Nazari da sharhi kan harkokin ilimi kwamred Yahaya Ungogo, ya ce yunkurin ‘yan majalisar dokokin ya yi daidai, amma batun rashawa da cin hanci da kuma cusa harkokin siyasa da ‘yan siyasar ke yi a fagen ilimi abin damuwa ne.
Sai dai Honarabul Kabiru Hassan Dashi ya ce majalisar dokokin Kano za ta sanya ido sosai domin kaucewa yanayin tsoma harkokin siyasa akan batun ilimi a jihar.
Ga Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:
Facebook Forum