Yayin da gwamnatin Najeriya ta sanar da aniyar samar da titin zamani da zai ratsa jihohin Kano, Jigawa da Katsina zuwa garin Maradi na Jamhuriyar Nijar kan kudi fiye da dala biliyan guda, domin ‘yan kasuwa da sauran kalubalen sufuri, batun ya sake kunno kai saboda alamar samun jinkiri.
Tun fiye da shekaru goma da suka gabata masu ababen hawa dake zirga zirga akan hanyar Kano, zuwa Babura a jihar Jigawa, zuwa Babban Mutum dake iyakar Najeriya da Jamuhuriyar Nijar ke kokawa game da lalacewar titin tare da jan hankalin hukumomin game da muhimmancin hanyar.
Hon. Nasiru Garba Dantiye tsohon wakilin yankin Babura a majalisar tarayya, ya ce, ya sha gabatar da batun wannan hanya a zauren majalisa, amma babu nasara, duk da kasancewar titin mallakar gwamnatin tarayya ne, gwamnonin jihohin Kano da Jigawa nada rawar takawa game da makomar titin.
Alhaji Idris Garba Unguwar Rimi, kwamishinan ayyuka na jihar Kano ya shaida wa wakilin muryar Amurka cewa, gwamnatin jihar Kano zata iya kokarinta wajen ganin ta gyara titin, amma iyakacin inda jihar ke da iko.
Dangane da yuwuwar hada gwiwa da gwamnatin Jigawa domin aiwatar da wannan aiki kuwa, kwamishinan ayyukan na jihar Kano ya ce, zasu bai wa gwamnan jihar Kano shawara domin tuntubar gwamnatin jihar Jigawa akan lamarin.
A farkon watannan na Oktoba gwamnatin Najeriya ta amince zata biya kimanin naira biliyan150 ga biyar daga cikin gwamnonin kasar bayan gudanar da wasu ayyuka na gwamnatin tarayya a jihohin su.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti:
Facebook Forum