Kimanin shekaru bakwai bayan kafa kwalejin maza zalla ta hadin gwiwa tsakanin hukumomin ilimi na Jamhuriyar Niger da gwamnatin jihar Kano a Najeriya, a bana ne ake sa ran yaye kashin farko na daliban kwalejin dake birnin Yamai, yayin da ake tsare-tsaren ci gaba da aikin makamanciyar ta domin dalibai mata a garin Zinder bayan da aikin gina ta ya samu tsaiko a shekarun baya.
Kyautata yaukin dangantaka da karfafa zumunci tsakanin al’umar Kano da na Jamhuriyar Niger, musamman ta fuskar al’adu, kasuwanci da zamantakewa, na daga muhimman dalilan kafa wannan kwaleji a birnin Yamai na Jamhuriyar Niger.
Makarantar sakandaren wadda ake koyo da koyar da darrussa a cikinta da harsunan Faransanci da Ingilishi, ana daukar dalibanta ne daga Kano da Nijar, bayan sun kammala makarantar Firamare kuma alhakin gudanar da ita ya rataya ne a wuyan gwamnatocin biyu.
Darektan kula da harkokin ilimi a ma’aikatar kula da makarantun sakandare ta Jamhuriyar, Nijar Malam Isa Namata, ya ce, suna fatan duk dalibin da ya kamala wannan makaranta zai iya ci gaba da karatun cikin harshen Faransanci ko Ingilishi ba tare da wata matsala ba.
A kokarin farfado da harkokin ilimi, hukumomin ilimin na Jamhuriyar Nijar da gwamnatin jihar Kano suna aiki tare don gina makamanciyar wannan kwaleji domin dalibai mata a garin Zinder.
Darakta a Ma'aikatar Ilimi ta Jamhuriyar Nijer, Mallam Isah Namata, ya ce rashin turo daliban da su ka cancanta daga jahar Kano ta Najeriya ya janyo matsalar ga wannan makarantar.
Kwamishinan ayyuka na Jihar Kano, Alhaji Idris Garba Unguwar Rimi, ya ce, gwamnati na dakon rahotan Injiniyoyin ma’aikatar dake aikin tantance yadda aikin gina kwalejin zai ci gaba.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Kwari cikin sauti:
Facebook Forum