Hauhawar hare-haren 'yan-bindiga a wuraren ibada ya sa kungiyar kiristoci ta kasa CAN, jawo hankalin rundunar 'yan-sandan jihar Kaduna kan adadin limamanta da 'yan-bindiga suka kashe cikin shekaru hudu.
Wasu daga cikin likitocin da suka kware a wannan fanni sun ce rashin fahimtar tasirin motsa jiki don kula da gabbai, yana matukar nakasa rayuwar mutane da dama a Najeriya.
Ganin yadda 'yan-bindiga ke neman sauya salo ta hanyar kai hare-hare wuraren ibada ya sa rundunar 'Yan-sandan jahar Kaduna kafa wani Kwamitin binciko musabbabin sabon salon harin don dakile shi.
Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da harin da wasu mahara dauke makamai a kan babura suka kai a gundumar Saya-Saya da ke karamar hukumar Ikara ta Jihar Kaduna, inda su ka kashe mutane a cikin masallaci a daren Juma'a.
Duk da sanar da samar da tallafin kudi da kayan abunci da gwamnatin tarayya ta yi don rage radadin kuncin rayuwa a Najeriya, Majalisar Malaman addinin Musulunci ta kasa ta ce tallafin ba zai yi wani tasiri ba.
Bayan karewar wa'adin da kungiyar ECOWAS ta baiwa Sojojin da su ka yi Juyin Mulkin Nijar, yanzu hankali ya koma kan taron da shugaban kungiyar ECOWAS, Shugaba Tinubu ya kira a ranar Alhamis.
Kwararru da masana na ci gaba da zakulo abubuwan da su ke ganin ka iya zama dalilan da, zuwa yanzu, suka hana amincewa da sunan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa'i a matsayin Ministan Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Al'ummar yankin Birnin Gwari sun ce akwai yuyiwar samun barazanar yunwa saboda manoma da dama sun kauracewa gonakin su sakamakon hare-haren 'yan-bindiga a yankin.
Duk da kai-komon da aka sha yi don baiwa sarakuna gurbi a kundin tsarin mulkin Najeriya ba tare da nasara ba, sabon shugaban majalissar wakilai a Najeriya, Hon. Abbas Tajuddeen ya ce za su dawo da kudin saka sarakuna cikin sha'anin mulki a kundin tsarin Mulkin Najeriya.
Domin Kari