Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda 'Yan bindiga Suka Kashe Mana Limamai 23 A Shekara Hudu - CAN


Kuniyar Kiristoci ta Najeriya CAN
Kuniyar Kiristoci ta Najeriya CAN

Hauhawar hare-haren 'yan-bindiga a wuraren ibada ya sa kungiyar kiristoci ta kasa CAN, jawo hankalin rundunar 'yan-sandan jihar Kaduna kan adadin limamanta da 'yan-bindiga suka kashe cikin shekaru hudu. 

Shugaban kungiyar kiristocin reshen jihar Kaduna, Rabaren Joseph John Hayab wanda ya yi jawabi a wani taron limaman coci-coci da kuma kwamishinan 'yan-sandan jihar Kaduna ya ce akwai bukatar jami'an tsaro su tashi tsaye.

A baya dai hare-haren 'yan-bindiga a wasu sassan jihar Kaduna ya hana manoma da 'yan-kasuwa da dama sukuni.

Sai dai duk da samun sauki yanzu 'yan-bindigan sun sauya salo ta yadda suka kai hari a wani masallaci da Saya-Sayan karamar hukumar Ikara da kuma wata majami'a fadan Kamantan a Kudancin Kaduna.

Shugaban kungiyar kiristoci na jihar Kaduna, Rabaren Joseph John Hayab ya ce alkalumman rayukan da suka halaka na da ban tsoro.

Rev John Joseph Hayab
Rev John Joseph Hayab

Duk da yake taron limaman coci-coci ne kan tsaro, kwamishinan 'yan-sandan jihar Kaduna CP Musa Garba ya ce masu kai hare-haren nan fa kowa ma kashewa suke ba tare da la'akkari da addini ko kabila ba.

Shi ma dai mai-magana da yawun majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci, Malam Abdullahi Bayero, ya ce tunkarar 'yan-bindigan kawai don kare kai shi ne mafita ga al'umar Najeriya.

Kafin tashi taron tsara tsarin tsarkake tsaron dai sai kwamishinan 'yan-sandan jihar Kaduna ya tabbatarwa da mahalarta taron cewa 'yan-bindiga da sauran bata-gari ba za su sami sakat a lokacin shi ba saboda haka ya nema al'uma su baiwa rundunar yan-sandan hadin kai wajen fallasa taba-gari.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG