Ganin yadda mutane da dama kan ci abin da suka ga dama kuma su ki kulawa da lafiyarsu, ya sa gwamnatin Jihar Kaduna ta nuna bukatar maida hankali wajen motsa jiki da kuma neman likitocin kashi don neman waraka ba tare da shan magani ba.
Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe wadda da ma likita ce, ta ce motsa jiki kadai zai iya magance cututtuka da dama ba tare da shan magani ba.
Mataimakiyar gwamnan, wadda kwamishiniyar lafiya, Dr. Umma Ahmed ta wakilta wajen taron ranar likitocin kashi da motsa jiki ta duniya da ya gudana a jami'ar jihar Kaduna, ta ce likitocin kashi za su sami dukkan goyon baya daga gwamnatin Jihar Kaduna.
Taken taron likitocin kashi da motsa jiki na bana dai shi ne, hanyoyin magance cututtuka ba tare da shan magani ba.
Shugaban kungiyar likitocin kashi da motsa jiki wadanda ba sa amfani da magani wajen magance cututtuka na jihar Kaduna, Dr. Bashir Sabo ya ce da yawan mutane ba su fahimci aikinsu ba.
Karancin likitocin kashi da motsa jiki dai na cikin manyan matsalolin da taron na bana ya tattauna.
Sai dai mataimakin shugaban jami'ar jihar ta Kaduna, KASU Prof. Abdullahi Musa ya ce, jami'ar na shirin magance wannan matsala ta hanyar ware kudi don kula da tsangayar karatun likitocin wannan fanni.
Wasu daga cikin likitocin da suka kware a wannan fanni sun ce rashin fahimtar tasirin motsa jiki don kula da gabbai na matukar nakasa rayuwar mutane a Najeriya.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna