KADUNA, NIGERIA - Jingine sunayen mutane uku cikin 48 da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai wa Majalissar Dattijai don tantance su a matsayin Ministoci dai ya bai wa wasu mamaki musamman ma dai tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasuru Ahmed El-rufa'in da ake ganin ya sami sassauci lokacin da Majalissar ta tantance shi.
Sen. Shehu Sani, tsohon ‘dan Majalisar Dattijai daga jihar Kaduna ya ce tabbas akwai wasu abubuwa da ka iya zama sanadin jingine tabbatar da Malam Nasuru El-rufa'i a matsayin Minista, kamar haddasa rikici tsakanin Ministocin da ake zarginsa da yi a baya, da kuma wasu furuce-furucensa.
Masana shari'a irinsu barista El-zubair Abubakar na ganin duk da abubuwan da ake tunanin jami'an tsaro sun rike a matsayin hujjar hana amincewa da sunan El-rufa'i a matsayin Minista, akwai yuwuwar daga baya ya tsallake.
Sai dai kuma farfesa Salihu Adamu Dadari na jami'ar Amadu Bello da ke Zaria ya ce bai ga wani abu cikin furucin tsohon Gwamna El-rufa'i da zai sa a hana shi Minista ba.
Dama dai wasu sun yi ta yada faifan bidiyo da ya nuna tsohon Gwamna Nasuru El-rufa'i na cewa kujerar Minista sai dai ya bar wa yara tunda ya taba yi a baya kuma ba wannan ne ma karon farko da tsohon Gwamnan ya samu matsala da 'yan Majalisar kasa ba, domin ya taba zargin su da neman toshiyar baki lokacin da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ba shi mukamin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja.
Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara:
Dandalin Mu Tattauna