Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Hadin Gwiwa Sun Yi Ikirarin Fatattakar Mayakan ISWAP A Yankin Tafkin Chadi


Sojojin Najeriya a wani aikin sintiri da suka yi (Facebook/ Nigerian Army)
Sojojin Najeriya a wani aikin sintiri da suka yi (Facebook/ Nigerian Army)

Dakarun kawancen Tafkin Chadi na ci gaba da mamaye tsibiran dake zama tungar 'yan ta'addan ISWAP a bangarorin Najeriya da Chadi.

Sojojin Najeriya da Chadi dake karkashin rundunar dakarun kmawancen kasashen nyankin Tafkin Tchadi, sun yi mummunar arangama da 'yan ta'addan ISWAP daga bangarorin Najeriya da Chadi a tsibiran dake zirin tafkin.

Wata sanarwa da kakakin rundunar Laftanar kanar Kamaruddeen Ademola Adegoke ya aikewa sashin Hausa na Muryar Amurka yace dakarun sunkai farmakinne inda suka sami nasarar isa har kangarwa dake yankin karamar hukumar kukawa a jihar Borno ta Bangaren Najeriya.

Mayakan wadanda suka mamaye zagayen yankunan Metele da Dogon Chuku inda suka yi gaba da gaba da mayakan ISWAP din aka yi kuma dauki ba dadi sosai inda kuma suka hallaka da dama daga cikin yan ta'addan kana wadanda suka rage kuma suka tsere.

Yayin dai wannan fafatawar sojin sun kwato manyan makaman atilari
wato motar babbar bindiga kirar Dushka da motar yaki, yayin da rundunar ta ce zata ci gaba da kai karin ire iren wannan farmaki a duk inda sansanonin yan ta'addan yake.

Su ma dakarun MNJTF shiyya ta uku sun kai samame a yankunan ‘yan
ta'addan ta bangaren kasar Chadi inda suka mamaye yankunan Tumbun
Fulani da Kudancin Arege inda a nan kuma aka kwato dimbin makamai.

‘Yan ta'addan dai yanzu sun fara yada farfagandar dake son zuguguta
irin karfi da tasirinsu cewa ya ma fi na dakarun kawancen ganin gwiwar
mayakan su ta yi sanyi suna ma kokarin ganin sun yi saranda sun bar
ta'addancin.

Babban kwamandan dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Chadin,
Janar AK Ibrahim na kara kira ga ‘yan ISWAP din da su yi watsi da
farfagandar shugabannin nasu su fito don yin saranda cikin girma da
arziki in ba haka ba kuma to duk wanda aka kama a filin daga to kuwa zai
yabawa aya zaki.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG