Biyo bayan taron da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi da manyan hafsoshin mayakan kasar tare da basu umarnin kawo karshen hauhawar aika aika na ‘yan ta’adda, da alamar dakarun sun fara motsawa.
A irin wannan hobbassa rundunar mayakan saman Najeriyar ta kai wani mummunan farmaki kan ‘yan ta’addan Boko Haram a dutsen Mandara dake Karamar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Bayanan da Wakilinmu ya tattaro na nuna cewa harin na Jirgin yaki yayi sanadin kashe wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram mai suna Alhaji Modu da mukarrabansa guda ashirin da bakwai.
Shi dai wannan babban kwamanda shi ne wanda a shekarar 2014 ya jagoranci wani harin da yai sanadin kashe daruruwan mutane a garin Bama tare da kwace ikon wurin inda suka maida shi abin da suka kira Daular Musulunci.
Wani babban Hafsa a rundunar mayakan kasar ya tabbatar wa Muryar Amurka cewa lallai kam jiragen yakin sun kai wannan farmaki amma cikakken karin bayani na tafe nan gaba a taron manema Labarai da hedkwatar tsaron kasar.
Masana daga yankin na arewa maso gabas irin su Dakta Abubakar M.S. na ganin wannan babban ci gaba ne a yaki da ta’addanci; zai kuma sa sauran yan ta’addan da basu mutu ba su yi saranda, ganin irin wannan farmaki ya sa kawo yanzu sama da yan Boko Haram dubu saba’in ne suka mika wuya.
Shi ma tsohon Hafsa a rundunar mayakan saman Iya Kwamanda (Air Commodore) Baba Gamawa ya nemi sojojin saman da su ci gaba da kai irin wannan farmaki akai akai ba kakkautawa don hanzarta maido da kwanciyar hankali a yankin.
Saurari Cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina: