An dai kame karin yan ta'addan ne a Omialarafa da ke karamar hukumar Ose a jihar Ondo. 'Yan ta'addan da aka kama sun hada da Al-Qasim Idriss, da Abdulhalim Idriss, Shi Abdulhalim kamar yadda rundunar tsaron tayi karin bayani shine wanda ya kitsa tare da jagorantar wani mummunan hari kan wani sansanin sojoji a jihar Kogi da ya yi sanadin hassarar rayuka,,,
Mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Manjo janaral Jimmy Akpor ya bayyana cewa, jami'an tsaron kasar sun cafke karin 'yan ta'adda biyu da ke cikin gungun maharan nan da suka hallaka gomman masu ibada a majami'ar Saint Francis da ke Owo.
Janar Akpor yace, yan sa'o'i kadan bayan da babban hafsan tsaron kasar Janar Irabor ya bayyana cafke yan ta'adda hudu na farko a jiya, hadin gwiwar sojoji da jami'an tsaron farin kaya na DSS sun kuma sake damke karin 'yan ta'adda biyu cikin maharan.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: