Jami'an hukumar sun shaidawa shugaban kasar cewa, bayan wannan farmaki kimanin daurarru dari takwas da saba'in da tara ne suka tsere. Koda yake Jami'an tsaro sun sake kamo guda dari hudu da arba'in da uku.
Duk da dai a halin yanzu daurarru dari biyar da hamsin da daya ne ke cikin gidan yarin mai cin mutane dari tara. Yayin da ake neman guda dari hudu da arba'in da uku da suka cika rigarsu da iska.
An shaidawa shugaba Buhari cewa fursunoni hudu sun rigamu gidan gaskiya yayinda karin wasu goma sha shida kuma suka Sami raunuka.
Ministan tsaron Najeriya Manjo Jabar Bashir Magashi ya shaidawa 'yan jarida cewa, suna jin yan ta'addan Boko Haram ne suka tafka wannan danyen aiki, domin akwai manyan kwamandojin Boko Haram da ake tsare dasu a gidan, da suka kai sama da sittin da dukansu suka cika rigarsu da iska.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: