ABUJA, NIGERIA - Wani da ya shaida lamarin wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilan tsaron, ya fada wa Muryar Amurka cewa jiragen yakin sun bude wa ‘yan ta’addan wuta ne a lokacin da suka tattaru a wani fili ranar Juma'ar data gabata a Jibularam da kuma Sabon tumbun ina suka kashe yawancinsu. Ya kara da cewa an yi imanin sauran wadanda suka tsira sun jikkata sosai.
Shelkwatar rundunar dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Chadi, a ta bakin Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim kwamandan rundunar, ta tabbatar wa Muryar Amurka cewa dakarunta na zafafa kai farmaki a sansanonin ‘yan ta'adda a kusan baki dayan yankin kuma zuwa nan gaba za ta fidda bayani a hukumance kan farmakin bayan ta kammala tattara alkaluma.
Farmakin na baya bayan nan ya ja hankalin kwararru irinsu, Abdulkarim Abbas, wanda ya ce sojojin sun gano logar yakin da ke taimaka musu wajen samun nasara.
Abbas ya ce shi ma gwamnan jihar Borno Babagana Zulum da kansa ya yi tsokaci kan wannan farmaki wanda ya ce yana daya daga cikin manyan nasarorin da dakarun suka cimma a tarihin yakin da su ke yi da ‘yan Boko Haram, yanzu har mutane na komawa garuruwansu.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina: