ABUJA, NIGERIA - Janar Yahya wanda ke magana yayin wani taro da manyan kwamandoji da Hafsoshi a birnin Abuja, ya ce dama sanannen abu ne sojoji suke bitar irin ka'idoji da tsarin rawar da suke takawa yayin gudanar da ayyukansu gwargwadon irin yanayi da halin da ake ciki.
Kuma wannan shi ne abin da ake yi don tabbatar da gudunmuwarsu ya taimakawa hukumomin fararen hula wajen samar da zabe na gaskiya mai cike da adalci.
Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriyar ya ce su fa ba su da alaka ta kusa ko ta nesa da ‘yan siyasa, muradinsu shi ne kawai samar da taimako ga hukumomin fararen hula, kana su koma gefe su ci gaba da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar masu.
Masana a Najeriya irinsu Farfesa Muhammed Tukur Baba ya ce lalle wannan bayani na babban hafsa abin ayaba ne saura kuma a baiwa sojin horo don tunkarar wannan aiki ba tare da nuna son kai ko wuce gona da iri ba.
Su ma ‘yan gwagwarmaya irinsu Comrade Kabiru Dakata na Cibiyar CAJA dake rajin samar da kyakkyawan shugabanci a Najeriya ya ce koda yake harkar samar da tsaro yayin zabe ba hurumin sojoji bane, amma duba da halin tsaro a kasa wannan ka iya zama dalilin shigowarsu cikin wannan sabga.
Amma duk da haka, Comrade Dakata ya ce akwai bukatar a baiwa sojojin horo na sanin abin da ya kamata su yi yayin zaben don gane cewar aikin ranar zabe daban yake da aikin da suka saba na yake-yake da sauransu, to wannan zai taimaka wajen kwantarwa fararen hula hankali.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Kaina: