Kakakin rundunar, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya shaidawa Muryar Amurka cewa irin wannan yunkuri ne da ya haddasa karancin kayayyakin bukatun yau da kullum ya sa 'yan ta'addan ke ta mika wuya ga dakaru.
Manjo Janar Edward Bouba ya ce “‘yan bindigan sun kashe hafsoshi guda uku ne da karin wasu zaratan mayaka 22 bayan kwanton bauna da maharan suka kaiwa dakarun da ya kai ga musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.”
Wani jirgin saman rundunar sojojin saman Najeriya ya yi hadari inda ya rikito a wani kauyen jihar Neja a ranar jiya Litinin.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce ta shirya tsaf don cika duk wani umarni da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai ba su na cika aiki.
Sojojin sun kuma gano tare da kone wasu haramtattun matatun mai da tankokin dakon mai shake da man sata.
Hakan ya biyo bayan matsayar da kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS ta cimma na cewa za ta dauki matakin soji idan har dakarun da suka yi juyin mulki a Nijar ba su mayar da kasar kan turbar dimokradiyya ba.
A ranar litinin din nan ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karawa babban hafsan sojin kasa, Taoreed Abiodun Lagbaja girma zuwa mukamin LAFTANAR JANAL mai tauraro uku.
A wani mataki mai kama da fifa-iya koma baya, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ba gudu ba ja da baya a yunkurin da ta ke yi na janye "yan sanda da ke ba da kariya ga wasu hamshakan mutane a kasar da ake kira VIP's.
Makonni kadan bayan barkewar cutar dabbobi ta Antrax a kasashen Ghana da Burkino Faso, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa cutar ta bulla a kasar.
Babban Hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, Manjo Janaral Taoreed Abiodun Lagbaja ya bayyana cewa yin ahuwa ko yafiya ba shi da wani tasiri a yaki da ta'addanci ko shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.
Ofisoshin Jakadancin Amurka da ke Abuja da Lagos sun gudanar da wani Kwas na wayar da kan daruruwan daliban Najeriya da su ka sami guraben karatu a jami'o'i da kwalejojin Amurka
Wasu munanan tagwayen hadurran mota ya lakume rayukan mutane uku a birnin Abuja.
Babban jami'in tsaro na ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya Brigediya Janar MATT MUNRO, ke bayyana haka yayin ziyara a hedkwatar rundunar ta MNJTF a birnin N''djamena dake kasar Tchadi.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce dakarun kasar da ke fafatawa a rundunar OPERATION HADIN KAI a arewa maso gabas sun yi wani kwantan bauna a kan iyakar Najeriya da kamaru, inda suka sami nasarar hallaka wasu mayakan Boko Haram biyar.
Ma'aikatar raya babban birnin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa an sami barkewar annobar cutar sarkewar numfashi na yara wato DIPHTHERIA a wasu yankunan birnin.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu a karon farko ya yi ganawar keke da keke da sabbin manyan hafsoshin kasar bayan nadinsu makonni biyu da suka shige.
Domin Kari