Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Yi Amai Ta Lashe


sufeta janar na 'yan sandan Najeirya, IGP Kayode Egbetokun
sufeta janar na 'yan sandan Najeirya, IGP Kayode Egbetokun

A wani mataki mai kama da fifa-iya koma baya, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ba gudu ba ja da baya a yunkurin da ta ke yi na janye "yan sanda da ke ba da kariya ga wasu hamshakan mutane a kasar da ake kira VIP's.

A cikin wata sanarwa da ya aikewa wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya ce sufeta-janar na 'yan sandan kasar IGP Kayode Egbetokun, ya kudiri aniyar janye 'yan sandan da ke aikin ba da kariya ga wasu rukunan manyan mutane da kamfanoni.

Sanarwar ta ce tuni har ma an fara janye 'yan sandan, yayin da nan gaba kadan kwamitin da aka kafa kan lamarin zai mika rahotonsa.

Sufetan na 'yan sandan Najeriyar a cewar sanarwar, tana son inganta rundunar kai daukin gaggawa wato “Police Quick Intervention Squard'' da tuni aka dau wannan mataki gabanin cimma janye 'yan sandan.

Matakin da ake sa ran zai karfafa aikin tabbatar da samar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a, a gefe daya kuma rundunar ta yi wani shiri na samar da kariya ga manyan mutanen da suka cancanci hakan.

To sai dai kuma a baya, rundunar 'yan sandan ta fidda sanarwa tana karyata batun janyewa manyan mutanen jami'anta da ke ba su kariya, abin da masu sharhi ke ganin tamkar ta yi amai ta lashe ne.

A ranar talata goma sha bakwai ga watan nan na Yuni ne kakakin rundunar 'yan sandan kasar ya fidda wata sanarwa inda yake karyata maganar janye jami'an da ke kare manya a kasar, inda ya ce tuni har an fara binciken inda wannan labari ya samo asali.

Sai dai kafin kwamitin ya kammala aikinsa sai ga shi kuma wata sanarwar mai cin karo da waccan, wacce a yanzu ta ke cewa za'a janye 'yan sandan daga aikin na kare manyan mutane.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG