Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burtaniya Za Ta Tallafawa Rundunar Kasashen Tafkin Tchadi

Burtaniya Ta Tallafawa Rundunar Kasashen Tafkin Tchadi
Burtaniya Ta Tallafawa Rundunar Kasashen Tafkin Tchadi

Babban jami'in tsaro na ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya Brigediya Janar MATT MUNRO, ke bayyana haka yayin ziyara a hedkwatar rundunar ta MNJTF a birnin N''djamena dake kasar Tchadi.

Gwamnatin Burtaniya ta ce za ta tallafawa rundunar dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Tchadi, wato MNJT/FMM, don ganin ta cimma makasudin da ya sa aka kafa ta.

Babban jami'in tsaro na ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya Brigediya Janar MATT MUNRO, ke bayyana haka yayin ziyara a hedkwatar rundunar ta MNJTF a birnin N''djamena dake kasar Tchadi.

Burtaniya Ta Tallafawa Rundunar Kasashen Tafkin Tchadi
Burtaniya Ta Tallafawa Rundunar Kasashen Tafkin Tchadi

Janaral Munro ya ce Burtaniya ta dau hanyar inganta alakar aiki tare da rundunar yankin gtafkin Tchadin, duba da irin dimbin muhimmancin da ta ke da shi na samar da zaman lafiya a yankin.

jami'in na Burtaniya ya ce ba tantama gudunmuwar za ta taka rawa wajen karawa rundunar ta MNJTF Kwarin gwiwa, musamman wajen tsare tsare da ma kaddamar da farmaki.

Da yake maida jawabi, mataimakin kwamandan rundunar tafkin Tchadin, Manjo Janar Assoulai Blama, ya nuna farin ciki ga gwamnatin Britaniya bisa irin dimbin goyon baya da tun tuni ta ke baiwa rundunar.

XS
SM
MD
LG