Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Najeriya 700 Sun Samu Guraben Karatu A Amurka


Dalibai da Amurka ta ba su gurbin karatu a Kasar
Dalibai da Amurka ta ba su gurbin karatu a Kasar

Ofisoshin Jakadancin Amurka da ke Abuja da Lagos sun gudanar da wani Kwas na wayar da kan daruruwan daliban Najeriya da su ka sami guraben karatu a jami'o'i da kwalejojin Amurka

ABUJA, NIGERIA - Kimanin daliban Najeriya dari bakwai ne su ka samu guraben karo karatu a Amurkan a wani shirin ba da tallafin karatu na gwamnatin ta Amurka mai suna EDUCATION USA, da ake sa ran nan gaba kadan za su tashi don tafiya Amurkan.

Dalibai da Amurka ta ba su gurbin karatu a Kasar
Dalibai da Amurka ta ba su gurbin karatu a Kasar

EDUCATION USA wani shirin ma'aikatar harkokikn wajen Amurka ne da ke marawa cibiyoyi dari hudu da talatin na daliban kasashen duniya da ke shiryarwa ne zuwa samun guraben karatu da ma bada tallafin karatun ga diyan talakawa da ba sa da sukuni

A bara dai kimanin daliban Najeriya dubu goma sha hudu ne su ka sami guraben karatu a jami'o'i da makarantu daban daban a Amurka da hakan ke nufin NAJERIYA ce kasa ta goma a duk duniya da dalibanta su ka fi samun guraben karatu a Amurka.

Jami'an diflomasiyyar Amurka sun yi fatan daliban Najeriyar da ake sa ran su zama manyan gobe, za su taimaka wajen bunkasa da kuma ci ban kasarsu a gaba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG