ABUJA, NIGERIA - A halin yanzu wasu rikakkun kwamandoji hudu da wasu zaratan mayakansu guda goma sha uku suka mika wuya ga sashe na uku na rundunar tafkin Chadin tare da iyalansu kimanin su arba'in da biyar.
Yan ta'addan wadanda suka mika wuya a garin Cross Kauna da ke yankin Baga a Arewa maso Gabashin Najeriya sun mika manyan bindigogi kirar AK 47 guda hudu da wata babbar bindiga kirar FN da harsasai kusan dari biyar.
Laftanar Kanar Abdullahi ya ce tun da farko a ranar goma sha hudu ga wannan wata wasu manyan kwamandoji biyu da wasu mayaka tara ne suka fara mika wuya da iyalansu ashirin da daya biyo bayan barin wuta da dakarun tafkin na Chadin suka yi ta yi ba kakkautawa.
Dakarun rundunar brigade ta goma sha tara da brigade ta dari hudu da uku ne su ka karbi ‘yan ta'addan da su ka mika wuya a Cross da Baga
Bugu da kari a ranar goma sha biyar ga wata ma wasu gaggan kwamandojin ‘yan ta'addan sun sake mika wuya da iyalansu ashirin da hudu tare da bindigogi kirar AK 47 da harsasai sama da dari bakwai da ma kudade.
Tuni dai masu bin diddigi akan al'amuran yankin tafkin Chadi ke ganin cewa wannan kan iya kaiwa ga kawo karshen tarzoma a yankin, kamar yadda Dr. Abubakar MS ya shaida wa Muryar Amurka, inda ya nemi jama'ar yankin da su baiwa dakarun hadin kai da goyon baya wajen kai musu bayanan sirri akan abubuwa da shirye-shiryen ‘yan ta'addan.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Dandalin Mu Tattauna