ABUJA, NIGERIA - Babban baturen Britaniya na ma’aikatar gona Dr. Vakulu ya ce an samu alamun cutar ne ta Anthrax a wani gidan gona da ake kiwon dabbobi dake garin Gajiri a karamar hukumar Sulejan Jihar Niger dake tsakiyar Arewacin Najeriya.
Dr. Columbia Vakulu na ma'aikatar gona da raya karkara ta Najeriya ya bayyana bullar cutar cikin wata sanarwar da ya rabawa manema labaru a Abuja inda ya ce wannan babban abin bakin ciki ne.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka da ya ziyarci garin ya gana da mai unguwar yankin na sabon garin Gajiri wanda ta tabbatar da bullar cutar da ke ta kashe shanu ba kakkautawa.
Ya ce suna binne shanun da suka mutu cikin rami don gudun kada a bari a samu yaduwar cututtuka a garin.
Da yake tsokaci akan cutar, tsohon shugaban likitocin dabbobi a Najeriya Dr. Ibrahim Ado Shehu ya bayyana cutar ta Anthrax a matsayin babbar cuta mai yin babbar illa ga dabbobi.
Likitan ya ce wannan cuta takan yadu kuma zuwa jikin bil'adama, don haka ya nemi ayi taka tsantsan don shawo kanta da wuri.
Tuni dai ma'aikatar gona da raya karkara ta Najeriya da hadin gwiwar hukumar kula da yaki da cutuka masu yaduwa ta kasa wato NCDC suka fara daukar matakan dakile cutar.
Baya ga haka an killace gonar da aka fara samun bullar cutar don kada cutar ta yadu zuwa sauran sassan jihar ko kasar.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:
Dandalin Mu Tattauna