Shugaban kasa muhammadu Buhari ya amince da karawa sufeto janar na 'yan sandan Najeriya Muhammed Abubakar Adamu Karin wa'adin watanni uku.
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta bankado wani yunkuri da wasu kungiyoyi ke yi, na tayar da rikicin kabilanci da na addini a kasar, ta hanyar kalaman tunzuri da raba kan al’umma.
Biyo bayan kiraye kirayen 'yan Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke manyan hafsan sojin Nnajeriya hudu. Bugu da kari, ya maye su da sabbi sannan ya masu ritaya.
Burtaniya ta sha alwashin taimaka wa dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Chadi wajen gaggauta kawo karshen mayakan kungiyar Boko Haram da take tafka ayyukan ta’addanci a yankin.
Kasar Chadi ta ce za ta hada kai da Najeriya wajen ganin an kawo karshen mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram da ke tafka aika aika a yankin.
A ci gaba da rangadin da ta ke yi a cibiyoyin tsaron Najeriya, sakatariyar harkokin sojin saman Amurka, Barbara Berrett ta jagoranci wata tawagar jami'ai biyar da suka gana da ministan tsaron Najeriya a birnin Abuja.
Da alamar su ma miyagun da ke gasa ma 'yan Najeriya aya a hannu sun kusa dandadawa, ganin yadda ake cigaba da kera ma Najeriya wasu jiragen yaki a Amurka, baya ga wasu matakan kuma da ake nazarin daukarsu.
Duba da yadda matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa ne ya sa Najeriya ta sayo wani sabon jirgin saman yaki mai saukar Ungulu da ake kira MI-171 E da kuma karin wani babban jirgin yakin jet mai suna L39- ZA don tunkarar matsalolin tsaro a shiyyoyin arewa maso gabas da arewa maso yammacin kasar.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zargi gwamnatin jihar zamfara bisa daukar nauyi tare da baiwa ‘yan bindiga dadi mafaka a yankinta.
Dubun biyu daga cikin mutanen da su ka sace wani Ba'amurke a Nijar su ka ketaro da shi Najeriya kwanan bayan ta cika. Hakan ya biyo bayan yinkurinsu na shirin daukar fansar kashe shida daga cikinsu da aka yi tun farko.
Biyo bayan rasuwar wani babban Janar na rundunar sojan Najeriya da ya halarci wani taro, gwaji ya nuna an sami karin wasu manyan hafsoshin kasar da suka kamu da cutar COVID-19.
A Najeriya, cutar COVID-19 ta halaka wani babban Janar din sojin kasar bayan da ya kamu da cutar wacce ake ganin farfadowarta a wasu sassan Najeriyar.
Biyo bayan nuna damuwa akan ayyukan ‘yan bindiga da jama'ar Katsina ke yi rundunar sojojin Najeriya ta ce ta na kara jan damara wajen yaki da ‘yan bindigar.
Bayan da rundunar ‘yan sanda ta kasa da kasa wato Interpol ta cafke Abdulrasheed Maina a kasar Nijar, a ranar 30 ga watan Nuwamba, ‘yan sanda sun tiso keyarsa inda suka kawoshi Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Yayin da yanayin tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya, Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauka daga mulki.
Ganin irin kashe kashen rashin imani da mayakan Boko Haram su ka yi ma manoma a Zabarmari, jahar Bornon arewacin Najeriya, an fara tafka muhawara kan shawarar dauko sojojin haya daga kasashen waje don agaza ma sojojin Najeriya.
Sababbin alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta fitar na nuna cewa kimanin mutum 110 ne mayakan Boko Haram suka yi wa kisar gilla a har na baya bayan na da ‘yan ta’addar suka kai a kusa da birnin Maiduguri.
Masana na ci gaba da yin tsokaci a kan yadda sha’anin tsaro ke kara tabarbarewa a arewacin Najeriya, lamarin dake neman gagarar jami’an tsaron kasar da ma mahukunta.
Yayin da miyagun cikin dajin Kaduna zuwa Abuja su ka sake dawowa da wani salo da kuntata ma matafiya, jama'a sun fara kiran da a yi bugun kwaf daya: a kwantar da komai na dajin a hutu.
Kasashe makwabtan Najeriya sun fara gane tasirin rawar da matasan sa-kai da ake kira Civilian JTF ke takawa wajen karya lagon ‘yan Boko Haram al'amarin da ya sa tuni wasunsu suka fara fito da nasu tsarin, wanda hakan kuma ke matukar taimakawa
Domin Kari