An bude wani taron kasa da kasa domin dakile hare haren Boko Haram a Birnin N’Djammena Kasar Chadi.
Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya ya yi karin haske kan soke rundunar ‘yan sanda ta musamman mai yaki da ‘yan fashi da makami wato “Special Anti Robbery Squad” ko SARS a takaice, wacce yanzu ana tsara kafa wata sabuwar runduna da zata maye gurbinta.
Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya dakatar da kan rundunar nan ta musamman mai yaki da ayyukan ‘yan fashi da makami, Federal SARS,
Tun bayan da ake samun karin haren-haren mayakan Boko Haram musamman wadanda suka rika kai wa akan gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Prof. Babanga Umara Zulum da wasu sassan kasar, muhawarar yin garanbawul ga fannin hafsoshin sojin kasar ta sake kunno kai.
Yayin da Najeriya ke fama da matsalar tsaro, wadda ta ke kuma shafar fannonin tattalin arziki da zamantakewa, sojojin kasar sun yi wani atisayen jiragen sama na bukin ranar samun 'yancin kai mai kama da nishadi da gargadi.
Yayin da kafafen yada labaran Najeriya ke ci gaba da yada labaran yiwuwar Minista Sadiya Umar Farouq ta auri Air Marshal Sadique, jama'ar gari kuma na ta fassara abin da hankulansu ke nuna masu.
A wani farmaki da wasu suka fassara a matsayin mayar da martani, dakarun Najeriya sun yi ikrarin kai wani samamen sama akan akan mabuyar mayakan Boko Haram da ke jihar Borno a arewa maso gabashin kasar, inda suka kashe wasu kusoshin kungiyar.
Wuni guda bayan jana’izar Kanar Bako, babban hafsan sojojin Najeriya ya jinjinawa kwmandan soji Kanar DC Bako da Mayakan kungiyar Boko Haram suka kashe
Rundunar sojojin Najeriya da ke kokarin shawo kan matsalar tsaro a kasar ta tarwatsa wani gungun ‘yan bindiga dadi a garin Adu da ke karamar hukumar Takum a jihar Taraba inda dakarun suka jikkata 'yan bindiga da yawa yayin da wasunsu suka tsere.
A wani al'amari mai kama da tauna tsakiuwa da kuma bayar da tabbaci, rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta tura manyan jami'anta don su jagoranci samar da wadataccen tsaro a zben gwamnan Edo.
A cigaba da kokarin fatattakar 'yan ta'adda da ke kai hare hare a dazukan jahar Kaduna, wasu jiragen yakin sun yi ta aman wuta a wasu wuraren buyar 'ya ta'adda a dazukan jahar Kaduna.
Ana kara samun haske kan ‘yan kungiyar ta'addan nan da aka tarwatsa a jihar Nasarawa dake arewa maso tsakiyar Najeriya.
Rundunar sojojin Najeriya tayi karin haske kan yan kungiyarta da aka tarwatsa a jihar Nasarawa cewa tun watanni shida da suka gabata suka rikide zuwa Boko haram
Rundunar dakarun kawance na kasashen tafkin Chadi, (MNJTF a takaice) ta kubutar da wani ma’aikacin jinkai da ya kwashe watanni takwas a hannun kungiyar ISWAP wadda ta yi garkuwa da shi.
Dakarun kawancen kasashen yankin Tafkin Tchadi sun rugurguza wani babban sansanin mayakan ISWAP dake Fedondiya a yankin Tunbun fulani a zirin tafkin na chadi.
Rundunar dakarun Kasashen yankin tafkin Chadi ta yi karin bayani dangane da yadda mayakan Boko Haram ke amfani da yara kanana a matsayin sojoji.
Kungiyar I.S. ta zartas da hukuncin kisa a kan wasu daga cikin manyan kwamandojinta a zirin tafkin Chadi, kamar yadda wata majiya mai karfi ta tabbatar wa VOA.
Baya ga fafatawa da mayakan ISWAP ke ci gaba da yi da dakarun Najeriya a Arewa maso gabas, yanzu kuma wata cacar baka ta barke tsakanin bangarorin biyu.
Masana harkar tsaro a Najeriya na ci gaba da jaddada tasirin da tattara bayanan sirri ke yi a yaki da masu ta da kayar baya musamman ma a arewa maso yammacin kasar yayin da sojojin Najeriya ke ci gaba da kai farmaki.
Domin Kari