Sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta tura wa Muryar Amurka, ta nuna cewa an yi wa wasu manyan hafsoshin sojan kasa da suka halarci wani babban taronsu su dari hudu da goma sha bakwai gwajin cutar.
A cewar Kanal Sagir Musa mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya, sakamakon gwajin ya nuna cewa kimanin hafsoshi ashirin da shida ne suka kamu da cutar, wadanda dukkanninsu an killacesu bisa ka'idoji da sharuddan yaki da cutar.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Muryar Amurka cewa cikin wadanda suka harbu da cutar har da wasu masu mukamin Janar su goma sha takwas.
A halin da ake ciki yanzu, ana ci gaba da gwajin cutar ta coronavirus ga dukkan hafsoshi da sojojin da ke aiki a shelkwatar sojin kasa ta Najeriya, a gefe guda kuma an yi feshin sinadarin kashe kwayoyin cuta a baki dayan ginin shelkwatar dakarun.