Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan sanda Sun Mayar Da Abdulrasheed Maina Najeriya


Abdulrasheed Maina
Abdulrasheed Maina

Bayan da rundunar ‘yan sanda ta kasa da kasa wato Interpol ta cafke Abdulrasheed Maina a kasar Nijar, a ranar 30 ga watan Nuwamba, ‘yan sanda sun tiso keyarsa inda suka kawoshi Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Cikin wata sanarwa da hedkwatar ‘yan sandan Najeriya ta fitar dauke da sa hannun kakakinta Frank Mba, wacce ta aikowa VOA ta nuna cewa a karshen makon jiya ne rundunar ta Interpol da kuma ‘yan sandan Nijar suka cafke shi a kasar ta Nijar, inda aka kawo shi cikin wani jirgi na ‘yan sandan.

In za a iya tunawa shi dai Abdulrasheed maina na fuskantar shari'ar da ke zarginsa da wawure kudaden ‘yan fansho lokacin da ya jagoranci wani kwamitin aiki da cikawa na shugaban kasa kan fansho.

A baya dai wata babbar kotu ta ba da belinsa wanda daga bisani ya tsere, lamarin da ya sa kotun ta tsare Sanata Ali Ndume - wanda ya tsaya masa aka ba da belinsa.

Rundunar ‘yan sandan race yanzu dai Abdulradhid maina zai ci gaba da fuskantar shari'a.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG