Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayani Kan Sabbin Manyan Hafsoshin Sojin Da Buhari Ya Nada


Manjo Janar Leo Irabor.
Manjo Janar Leo Irabor.

Biyo bayan kiraye kirayen 'yan Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke manyan hafsan sojin Nnajeriya hudu. Bugu da kari, ya maye su da sabbi sannan ya masu ritaya.

Kamar yadda ba a rasa ji ba, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sauke mayan hafsoshin sojin Najeriya hudu ya kuma yi masu ritaya daga aiki, ya maye gurbinsu da sabbi.

Manyan hafsojin sun hada da Babban Hafsan Tsaron Kasa, Janar Abayomi Olonisakin; da Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftana Janar Tukur Buratai; da Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal (Air Marshal) Sadique Abubakar; da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas.

Sabbin manyan hafsoshin sojin da aka nada sun hada da Janar Leo Irabor, a matsayin Babban Hafsan Tsaron Kasa; Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, a matsayin Babban Hafsan Ssojin Ruwan Najeriya; Janar I. Attahiru, Babban Hafsan Sojin Kasa Na Najeriya da kuma Iya Mashal (Air Marshal) Isiaka. O. Amao, Babban Hafsan Sojin Sama.

An haifi sabon Babban Hafsan Tsaron Kasa, Janar Leo Irabo ne ranar 5 ga watan Oktoban 1965, a Karamar Hukumar Ika Ta Kudu da ke jahar Delta ta kudu maso kudancin Najeriya. Ya samu digiri na biyu har guda biyu daga Jami’ar Ghana da ke Accra da Jami’ar Kwararru Ta Bangladesh; sannan ya samu horo a matsayin Injiniya a Jami’ar Obafemi Awolowo, Najeriya.

Cikin mukaman da ya taba rikewa har da na Babban Kwamandan Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram. Daga nan ya zama Babban Kwamandan Rundunar Dakarun Hadin Gwiwa Na Kasashe Ma’abuta Tafkin Chadi da ke yaki Boko Haram. Kafin nadinsa na yanzu, shi ne Babban Kwamandan Rundunar TRADOC ta sojin Najeriya da ke Minna, Jahar Naija.

Shi kuma sabon Babban Hafsan Sojin Kasa Na Najeriya, Majo Janar Ibrahim Attahiru, an haife shi ne ran 10 ga watan Afirilun 1966 a Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa a Jahar ta Kaduna. Ya rike mukamin Babban Kwamandan Operation Lafiya Dole mai yaki da kungiyar Boko Haram a shekara ta 2017. Kafin nadinsa na yanzu shi ne Babban Kwamandan Runduna Ta 82 Na Sojojin Najeriya.

Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, Babban Hafsan Sojin Ruwan Najeriya, shi kuma an haife shi ne a Karamar Hukumar Nasarawa ta jahar Kano, a ranar 24 ga watan Satumban 1966. Ya kammala makarantar sojoji ta NDA a shekarar 1988 kuma ya kasance daga cikin sojojin da ke yaki karkashin ruwa. Ya halarci kwasa kwasai da dama a ciki da wajen Najeriya. Kafin nadinsa na yanzu darakta ne a Hukumar Kula Da Tsaron Sararin Saman Najeriya.

Sannan shi kuma Iya Mashal (Air Marshal) Isiaka O. Amao, Babban Hafsan Sojin Sama, an haife shi ne a garin Enugu, amma iyayensu ‘yan asalin Karamar Hukumar Oshogbo ne ta jahar Osun. Ya fara aikin soji a 1994 bayan kammala makarantar NDA. Ya halarci kwasa kwasai a Najeriya da kuma kasashen Indiya, China da Pakistan. Iya Mashal Amao, wanda kwararren mayakin babban jirgin yaki ne, ya taka rawa a yake yaken da aka yi a kasar Mali da na Boko Haram da sauran fafatukan tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina ta sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

Karin bayani akan: Buratai, Janar Leo Irabor, Isiaka Amao​, Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG