Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin Jirgin Saman Sojan Najeriya Ya Kashe Mutum 7


Hadarin Jirgin Saman Najeriya
Hadarin Jirgin Saman Najeriya

Hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya ta tabbatar da cewa wani jirginta ya yi hatsari a ranar Lahadi kuma jami'anta 7 sun mutu.

Jirgin wanda ya tashi da nufin zuwa Minna a jihar Neja ya juyo bayan da injinsa ya samu tangarda wanda kuma ya samu hadarin lokacin da yake kokarin sauka.

Sai dai dukkannin mutune bakwai da ke cikin jirgin sun mutu nan take.

A cikin wata takaitacciyar sanarwa da ya aikewa VOA, kakakin rundunar sojan saman Najeriya, Air Vice Marshall Ibikunle Daramola, ya ce jirgin mai suna NAF BEECHCRAFT KingAir B350i ya samu hadarin ne sakamakon tangardar inji, yayin da yake sauka a filin jirgin saman Abuja.

Hadarin Jirgin Saman Najeriya
Hadarin Jirgin Saman Najeriya

Wani da ya shaida aukuwar hadarin ya ce jirgin ya yi ta tangal tangal a lokacin da yake yin kasa kafin daga bisani ya fado kan wata bishiyar mangwaro kusa da wani rafi da ke kauyan Basa.

Tuni dai babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya, Air vice marshal Isiyaka Amao, ya bada umarnin kaddamar da bincike don gano musabbabin aukuwar hadarin.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG