Air Marshall Sadique Abubakar ya ce a halin da ake ciki, tuni jiragen yakin suka shafe sa'o'i dubu talatin da bakwai a sama, can a filin daga a arewa maso gabas. Bayan sabbin jiragen yakin, yanzu akwai karin wasu jiragen guda ashirin da uku da basa aiki a baya amma yanzu duk an gyarasu kuma suna can a fagen fama.
A shekara ta 2015, kashi 35 cikin 100 na jiragen yakin Najeriya ne kadai ke tashi amma yanzu kimanin kashi 85 ne ke tashi suna kuma aiki sosai.
Duba da irin wannan ci gaba da aka samu ana sa ran kawo karshen 'yan ta'adda da 'yan boko haram a Najeriya.
Ministan tsaron Najeriya Bashir Salihi Magashi, ya ce sun sha fadin cewa in Allah ya yarda sojojin Najeriya sun fi karfin 'yan ta'addan da ke kasar, abinda dai kawai basu sani ba shi ne lokacin da za a gama wannan yakin. Ya kara da cewa a shirye suke su yaki duk wasu tsagera ba ma 'yan boko haram ba kadai a Najeriya.
A cewar masanin tsaro, Wing Commander Musa Isa Salmanu, duk da cewa yakin sunkuru ba a iya cewa ga lokacin da za a gama shi, amma a iya cewa ga lokacin da za a ci karfinsa.
Saurara karin bayani a sauti: