Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Tsaro: Kungiyar Dattawan Arewa Na Kiran Buhari Ya Sauka


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Yayin da yanayin tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya, Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauka daga mulki.

Bayan munanan hare hare na baya bayan nan a arewacin Najeriya, Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari da
ya sauka daga mukaminsa saboda yadda yanayin tsaron kasar ke ta cigaba da tabarbarewa.

Kakakin kungiyar, Dr Hakeem Baba Ahmed ya shaida wa Muryar Amurka cewa lalle Shugaban Kasa Buhari harkar tsaro ta zubuce masa, kuma ba zai iya tsare yan Najeriya ba, ko kuma bai son tsare su, ganin yadda kasar ke ciki game da batun tsaro.

Dr. Hakeem Baba-Ahmed
Dr. Hakeem Baba-Ahmed

Dr, Hakeem ya ce a baya shi kansa Shugaba Buhari ya taba cewa Shugaban

da ya gada wato Goodluck Jonathan ya yi murabus saboda matsalar tsaro a
wancan lokacin, saboda haka shi ma, tunda yanzu ya gaza, to ya sauka.

Dattawan na arewa sun ce Buhari baida wani zabi illa kawai ya yi murabus ganin ya gaza sauke amanar da ya dauka musamman a halin da kasar ta sami kanta a halin yanzu na balbalcewar tsaro.

A cewar masanin tsaro a Jami'ar Maiduguri duk fa laifin tsaron nan ya
ta'allaka ne akan Shugaban kasa duba da yadda yake rikon sakainar
kashi da batun na tsaron rayukan jama'a.

Kungiyar Dattawan Arewa
Kungiyar Dattawan Arewa

Dr Dongel ya ce shi bai ga laifin sojoji ba, don shi ne babban kwamandan
askarawan kasar, don haka dayan abu uku ne, kodai Shugaban bai ma san halin da tsaron ke ciki ba ko ana mai karya ne akan yanayin tsaron ko kuma ya gaza, ta yadda duk wani abu da yakamata a gaya wa Shugaban an gaya mai amma ba abin da ya canza.

Shi kuwa Zanna Boguma na Borno, Alhaji Zanna Hassan Boguma ya ce tunda abin ya kai haka, to akwai bukatar Shugaba Buhari ya nemi dauki daga kasashen waje don kawo karshen matsalar tsaron.

Dayake maida martani, daya daga cikin masu magana da yawun Shugaban
kasar, Alhaji Bashir Ahmed, ya ce Shugaba Buhari na iya kokarinsa kan
batun na tsaro kuma halin da ake ciki ma na yanzu zai wuce, don haka
Shugaban ba zai yi murabus ba.

Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


XS
SM
MD
LG