Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitaccen Tarihin Manjo Janar Farouk Yahaya


Manjo Janar Farouk Yahaya (Twitter/@HQNigerianArmy))
Manjo Janar Farouk Yahaya (Twitter/@HQNigerianArmy))

Manjo Janar Yahaya, ya rike mukamai da dama ciki har da Kwamandan rundunar tsaro ta Briged da kuma mukamin Darekta a kwalejin sojoji ta AFSC.

An haifi sabon babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriyar, Manjo
Janaral Farouk Yahaya ranar 5 ga watan Janairun 1966, a Sifawa
dake yankin karamar hukumar Bodinga dake Jihar Sokoto a arewa maso
yammacin Najeriya.

Janaral Yahaya wanda mamba ne na kwas na 37 na makarantar horas da
Hafsoshin Najeriya (NDA) ya fara samun horo na CADET a ran 27
bakwai ga watan Satumba 1985, bayan ya kare ya fara aiki a sojojin
dake bangaren sojojin Infantry, wato masu yaki gaba da gaba ranar 22
ga watan Satumbar 1990.

Janaral farouk ya yi aikace-aikace da dama a gidan soji kadan daga ciki
shi ne kwamandan Garrison na Birged din mayakan dake kula da tsaron
fadar shuganan kasa, ya kuma koyar a kwalejin horas da manya-manyan
hafsoshin sojojin Najeriya wato Armed Forces Command and Staff College.

Ya kuma rike mukaddashin Darakta a ofishin sakataren rundunar sojin
Najeriya da kuma sashen bincike.

Karin bayani akan: Janaral Farouk Yahaya, Boko Haram, Niger Delta, Nigeria, da Najeriya.

Ya kuma rike mukamin shugaban ma'aikata a rundunar hadin gwiwa dake
aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Niger Delta wato Operation Pulo
Shield. Bugu da kari, ya kuma yi babban jami'i a ofishin ministan tsaron
Najeriya sannan ya yi kwamandan Birged na 4 a rundunar Operation Zaman
lafiya ya kuma yi darakta na ma'aikata a hedkwatar sojojin Najeriya.

Daga nan likkafa ta yi gaba, aka nada shi sakataren rundunar sojojin
Najeriya sannan an nada shi babban kwamandan runduna ta daya na
sojojin Najeriya, daga inda kuma daga nan aka nadashi babban
kwamandan rundunar yaki da Boko Haram wato “Theartre Commander, Operation Lafiya Dole” wacce yanzu ta zama “Operation Hadin Kai.”

XS
SM
MD
LG