Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Za Ta Kara Jiragen Ruwan Yaki Don Tunkarar Tsaro


Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen kara samarwa mayakan ruwan jiragen ruwan yaki da ma sauran kayayyakin aiki, don kara tunkarar matsalar tsaro gadan gadan.

Yanzu haka ma dai wata tawaga mai karfin gaske da ta kushi jami'ai daga ma'aikatar tsaro da hedkwatar sojin ruwa na kan hanyarsu zuwa birnin Paris inda za a karbo wani jirgi na musamman mai suna NIGERIAN NAVY SHIP PLANNER wanda za a yi amfani da shi wajen kididdiga da bayanin sifofi da yanayin karkashin ruwa don kara bunkasa tsaro.

Bugu da kari, bayan karbar sabon jirgin, tawagar kazalika zata kuma sa hannu don kerawa Najeriya wani karin jirgin makamancin wanda za a karbo, kuma a cewar kakakin hedkwatar rundunar sojojin ruwan Najeriya, Navy Commodore Sulyman Dahun.

Commodore Dahun yace cikin shekaru biyar da suka gabata, gwamnatin Tarayya ta samarwa sojojin ruwan kimanin jirage dari uku da tamanin irin wadanda za a iya sintiri dasu sannan ayi yaki da su.

Karin bayani akan: Commodore Sulyman Dahun, NAVY, Shugaba Muhammadu Buhari, Guinea, Nigeria, da Najeriya.

Baya ga tunkarar matsalolin tsaro a cikin ruwan Najeriya, gabar tekun Guinea shi ma na fama da kalubalen tsaro da sauran manyan laifuka a cikin teku al'amarin da yaja hankalin shugabannin Afirka akai wani taron tsaro na euwa a birnin Younde.

Navy Commodore Sulyman Dahun yace a wannan taro an cimma yarjejeniya da neman kkasashe hudu da ke makwabtaka da juna su yi hadin gwiwa don aiki tare na yiwa tufkar hanci

Maganar tsaro a gabar tekun Guinea a cewar kakakin mayakan ruwan abu ne dake damun gwamnati da sojoji, amma a gaba daya in an duba daga shekara ta 2016 zuwa yanzu an ci karfin matsalar duk da cewa akan fuskanci damuwa jifa jifa.

kwararre kan tsaron ruwa, Comrade Abubakar Abdulsalam yace bisa irin nazarinsu a iya cewa sojojin ruwan Najeriya sun ci gagarumar nasara akan yan fashin teku da masu safarar mutane akan teku.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG