Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Karbi Jiragen Yakin A29 Super Tucano Daga Amurka


Jiragen A29 na Super Tucano.
Jiragen A29 na Super Tucano.

A hukumance, Amurka ta mikawa Najeriya manyan jiragen yakin nan na zami wato A29 Super Tucano a wani dan kwarya-kwaryan biki da aka yi a sansanin sojojin saman Najeriya dake filin jirgin saman birnin Abuja.

Da yake jawabi a wajen mikawa Najeriya jiragen yakin, babban kwamandan dakarun saman Amurka dake kula da Turai da Afirka Janaral Jeff Harrigian ya ce mika wadannan jirage na nuni da irin kyakkyawar alakar aiki tare dake tsakanin Amurka da Najeriya.

Wani bangare na wannan alakar shi ne Amurka za ta horas da dakarun Najeriya batun mutunta ‘yancin bil'adama, ana sa ran wadannan jiragen yaki na zamani za su taka rawa wajen tunkarar aika-aikar ‘yan ta'adda.

Jiragen yakin na Super Tucano wadanda aka yi masu kyakkyawan tsarin sadarwa da sojojin kasa da sojojin ruwa, Amurka ta kuma hado da kayayyakin gyaransu na tsawon shekaru ko da za a bukaci hakan sannan za ta sa hannu wajen kara inganta wuraren ajiyar jiragen daka sansanin jiragen saman mayakan Najeriya dake Ka'inji.

Kimanin Dalar Amurka milyan dari biyar ne Najeriya ta kashe wajen sayowadannan jirage kudade mafi yawa da wata kasa a Nahiyar Afirka ta Kudu da hamadar Sahara ta taba kashewa wajen samar da jiragen yakin.

Babban kwamandan dakarun saman Amurka dake kula da Turai da Afirkan ya ce ba ko tantama wadannan jirage zasu taimaka wajen fatattakar ‘yan ta'adda musamman ganin jiragen na dauke da makaman da in an harbasu basa kuskurewa.

Ministan tsaron Najeriya da babban hafsan tsaron Najeriya ne suka karbi jiragen yakin a madadin gwamnatin kasar. Kimanin matuka jiragen sojin saman Najeriya sittin da ukune Amurka ta horas wadanda zasu sarrafa wadannan jirage samfurin A 29 Super Tucano.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne irin tasirin da wadannan jirage za su yi wajen samar da tsaro a kasar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Kaina:

Najeriya Ta Karbi Jiragen Yakin A29 Super Tucano Daga Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00


TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG