Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paparoma Francis Ya Yi Tsokaci Dangane Da Matsalolin Tsaro Da Ya Addabi Najeriya


Paparoma Francis ya bayyana takaici kan matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta ya kuma bayyana niyar bada gudummuwa domin shawo kan matsalar.

Da yake tarbar sabon jakadan Najeriya a fadarsa, Paparoman ya yaba da Irin kwazon gwamnatin shugaba.Muhammadu Buhari na shawo kan matsalar. Ya ce matsalar tsaro yanzu ta zame ruwan dare inda ya sha Alwashin daukar lokaci ya yiwa Najeriya addu'a ta musamman.

Jagoran darikar katolikan na duniya yace rawar da gwamnatin Najeriya ke takawa wajen yiwa tufkar hanci lalle abin a yaba ne.

Tuni dai jagororin addinin kirista a Najeriya irinsu Reverand Dr. David Chasa su ka yi maraba da wannan dauki na Paparoma.

Ya ce ko da yake dama suma suna addu'a, amma manyan mutane irin su Paparoma su shigo cikin maganar lalle abin a yaba ne.

Suma jama'ar yankunan dake fama da kalubalen tsaro irinsu Ibrahim Janyau fake zama jagoran wata kungiyar dake fafutikar neman zaman lafiya a jihar zamfara mai fama da tashin hankali, sun yi na'am da wannan dauki na paparoma, suna masu nuna gamsuwa da kuma farin ciki ganin an tuna da halin da suke ciki.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG