Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Gudanar Da Bikin Ranar Sojoji A Najeriya


Bikin Ranar Sojoji
Bikin Ranar Sojoji

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana bikin Ranar Sojoji a matsayin wani abin da ke ci gaba da baiwa 'yan kasa kyakkyawan fata da kwarin gwiwa a hankoronsu na rayuwa cikin zaman lafiya irin na al'umar dake rayuwa karkashin tsari na dimokradiyya.

Rundunar sojin Najeriya wacce ke da dogon tarihi na shekaru dari da tamanin da biyar da ta somo daga turawan mulkin mallaka, ta taka rawa ta musamman a yakin duniya na farko da na biyu da kuma yakin basasar hada kan Najeriya.

Bikin Ranar Sojoji
Bikin Ranar Sojoji

Shugaba Buhari wanda ministan Tsaro Bashir Magashi ya wakilce shi, ya ce gwamnatinsa na sane da irin nasarori da rundunar sojin Najeriya ke samu na zuwa ne da irin nasa kalubale, domin wasu sojojin sun rasa rayukansu, wasu sun sami raunuka wasu kuma sun dade ba sa tare da iyalansu, inda ya bukaci dakarun da su kara zage damtse wajen bullo da sabbin dabaru da salon kara tunkarar kalubalen tsaro.

Bikin Ranar Sojoji
Bikin Ranar Sojoji

Tun da farko cikin jawabinsa, Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahya ya yi bayani kan salsalar bikin.

Janar Yahya ya ce duba da irin rawar da sojojin suka taka wajen kawo karshen yakin ya sa aka kebe irin ranar kowane shekara don bitar yanayi da halin da dakarun suke ciki a kuma tsara yadda za a tunkari gaba.

Bikin Ranar Sojoji
Bikin Ranar Sojoji

Bikin na wannan rana wanda aka karkare da lakcoci da kuma karrama rukunan sojoji da Hafsoshi ashirin da suka yi fice a fagen daga irinsu Magatakardar Makarantar da Hafsoshin soji ta NDA, Brigediya Janar Auwal Mamuda Gumel da a lokacin da yake Kwamandan wani Brigade a Arewa maso gabas ya jagoranci fatattakar 'yan ta'addan Boko Haram tare da hadin gwiwar sojin Kamaru a wani farmaki mai take "Operation Rufe Kofa."

Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Kaina:

Yadda Aka Gudanar Da Bikin Ranar Sojoji A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00


XS
SM
MD
LG