Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Nemi Taimakon Dakarun Ruwan Najeriya


Wasu manyan dakarun ruwan Najeriya.
Wasu manyan dakarun ruwan Najeriya.

A wani yunkurin shawo kan matsalar tsaro dake kara tabarbarewa a gabar tekun Guinea, rundunar sojojin ruwan kasar Ghana ta nemi agaji daga takwararta ta Najeriya don shawo kan matsalar.

Da yake jawabi a hedkwatar rundunar mayakan Ruwan Najeriya a Abuja,
Babban hafsan Hafsoshin mayakan Ruwan kasar Ghana Rear Admiral Issa
Adam Yakubu, ya ce shugaban kasarsu Nana Akuffo Ado ne ya umarcesu da su gana da rundunar mayakan ruwan Najeriya don ganin yadda za a tunkari
matsalar tsaro dake kara mamaye gabar tekun Guinea.

Ya ce bisa la'akkari da karfin mayakan ruwan Najeriya, a matsayinta na
babbar yaya, lalle suna da yakinin za ta iya jan gabarar tabbatar da
tsaro a yankin don haka Ghana na fatan Najeriya za ta samar da mafita.

Karin bayani akan: sojoji, tekun Guinea, Ghana, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Ya kara da cewa, idan ka tsare gidanka alhali gidan makwabcinka na ci da
wuta to baka tsira ba.

Tun da farko cikin nasa jawabin, babban Hafsan Hafsoshin mayakan ruwan
Najeriya Vice Admiral Auwal Gambo, ya yi bayanin cewa gabar tekun Guinea
a halin yanzu na kara fuskantar tabarbarewar tsaro sakamakon karancin
dakarun ruwan da za su tsare yankin.

Admiral Gambo ya ce hakan ne kuma ke kara ta'azzara farfado da kalubalen
tsaro kamar fashin teku, garkuwa da mutane a ruwa da kuma kai hare-
hare a muradan tattalin arziki da ma jiragen ruwa, inda Admiral Gambo
ya yi fatan taron zai samar da hanyar da za a bi don shawo kan matsalar a
gaba daya.

Masana tsaron ruwa irinsu Comrade Abubakar Abdulsalam na ganin wannan
yunkuri ya zo daidai lokacin da ya dace musamman ganin Najeriya a babbar
kasa ce wacce ta fi duk kasashen yankin karfin sojan ruwa da ma na kasa
da na sama.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:

Ghana Ta Nemi Taimakon Dakarun Ruwan Najeriya - 3'10"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG