A yayin da kungiyar dattawan arewacin Najeriya ke ci gaba da jaddada matsayinta na cewa ba za a tilasta wa ‘yan yankin arewa siyasar karba-karba na dole ba, su ‘yan kudu ma na zaune daram kan matsayinsu na mayar da shugabancin Najeriya bayan mulkin shugaba Buhari yankin na su.
"Tun da akwai yawan jama’a da ake bukata a zabe, babu wani dalili da zai sa Arewa ta tsaya a mataki na biyu alhalin za ta iya neman matakin farko kuma ta sami nasara."
Bayan ba da umarnin yi wa kamfanin mai na Najeriya na NNPC rijista a matsayin kamfanin kasuwancia, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin shugabanni da za su jagorance shi.
Ministan kwadago da samar da aikin yi na Najeriya Chris Ngige ya roki kungiyar likitoci masu neman kwarewa na kasar da ta mutunta umarnin kotu na dakatar da yajin aikin da suke yi, a yayin da gwamnatin ke ci gaba da tattaunawa da kungiyar don kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu.
Majalisar harkokin shari’a a Najeriya ta duba jerin sunayen alkalai da ma’aikatan shari’a da kwamitin daukan aikinta ya gabatar mata kuma ta yanke shawarar amincewa da jami’ansu 37.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta bayyana cewa ta fara kamen yan kasar da ke karbar kudadden kasashen waje a bankuna da sunan fita kasashen waje kasuwanci, neman lafiya, karatu da sauran su da bizar bogi.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa a shirye take ta janye karar da ta shigar a gaban kotun kan kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasar wato NARD, idan har likitocin masu yajin aiki suka koma bakin aikinsu.
Bayan 'yan sa’ao’i da sace wani dan majalisar dokokin jihar Katsina, wasu ’yan bindiga sun kai hari a kauyen Tafoki na karamar hukumar mulkin Faskari, inda suka yi awon gaba da kanwar mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Shehu Dalhatu Tafoki.
Wasu 'yan Najeriya sun ce ba su gani a kasa ba, bayan Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa shugaba Buhari ya bullo da manufofi, dokoki, da gudanar da muhimman ayyukan da kuma kammala wasu tun lokacin da ya dare kan karagar mulki a shekarar 2015.
Kungiyar dattawan Arewa ta ce umarnin rurrufe hanyoyin sadarwa da matakan rufe kasuwanni da makarantu a jihar Zamfara ba ita ce mafita ga ayyukan yan bindiga ba, a daidai lokacin da jama'ar jihar suke bayyana cewa matakan sun soma haifar da kyakkyawan sakamako.
Duk da hukuncin wata babbar kotu dake da zama a birnin Asaba na Jihar Delta da ya dakatar da jam’iyyar APC daga shirya tarukan ta na gobe asabar, jam’iyyar ta ce tana nan kan bakan ta na gudanar da tarukan.
Ministan hukumar kula da yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa a halin yanzu akwai ayuka sama da dubu 13 da aka yi watsi da su a yankinsa.
Hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta Najeriya wato SEC ta bayyana cewa ta yi asarar Naira biliyan 9 a cikin shekaru ukun da suka gabata sakamakon matsin tattalin arziki.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kisan dan sanata Bala Na’Allah mai wakiltar mazabar Kebbi ta kudu, Kyaftin Abdulkarim Ibn Na’Allah.
Gwamna Simon Lalong na jihar filato ya sassauta dokar hana fita da ya saka a wasu sassa na jihar kamar garin Jos da Bassa sakamakon rikicin da ya barke a jihar da ya haifar da rashin tsaro.
Ma’aikacin gidan talabijan na Channels, Kayode Okikiolu, ya musanta labarin cewa hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta kama shi da abokin aikinsa Chamberlain Usoh a ranar Alhamis.
Faifan Bidiyon Kayode Okikiolu
‘Yan bindigan da suka yi awun gaba da yaran islamiyyar ta garin Tegina dai sun rike yara a tsawon kwanaki 88 kafin suka sako su da maraicen jiya Alhamis.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi nuni da cewa gwamnati na yin wani shiri cikin sirri mai taken Sulhu, wanda aka tsara don fitar da kwamandojin kungiyoyin 'yan ta'adda, da suka hada da Boko Haram da ISWAP daga cikin dazuzzuka, gyara su da samar musu da sabbin hanyoyin rayuwa.
Gabanin babban taron jam’iyyar PDP, rikicin cikin gida na kara tsananta a cikin jam'iyyar a yayin da shugaban jam’iyyar Uche Secondus ya yi kememe cewa ba zai bar kujerarsa ba har sai ya kamalla wa’adinsa na shekara 4.
Domin Kari