Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Kashe Dan Sanata Bala Na’allah A Gidansa Dake Malali


Marigayi Kyaftin AbdulKarim Na'Allah.
Marigayi Kyaftin AbdulKarim Na'Allah.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kisan dan sanata Bala Na’Allah mai wakiltar mazabar Kebbi ta kudu, Kyaftin Abdulkarim Ibn Na’Allah.

‘Yan sandan jihar Kaduna dai sun bayyana cewa wasu da ake zargin maharan 'yan bindiga ne suka shake marigayi Kyaftin Abdulkarim Ibn Na’Allah har lahira.

Marigayi kyaftin Abdulkarim matukin jirgin sama ne wanda maharan suka kashe a gidansa a ranar Asabar a jihar Kaduna, kuma yana da shekaru 36 a duniya kafin mutuwarsa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya fitar ta ce maharan sun yi nasarar shiga gidan marigayi Abdulkarim da ke kan titin Umar Gwandu a unguwar Malali na garin Kaduna cikin dare inda suka hallaka shi.

Haka kuma, sanarwar ta kara da cewa maharan sun yi awon gaba da motar marigayin kirar Lexus SUV baya sun kashe shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya kuma ce jami’an rundunarsa sun fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin, da nufin bankado wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Haka kuma rundunar ta bukaci jama’a su taimaka da bayanai da za su kai ga bankado maharan tare da dakile sake faruwar irin wannan mummunan lamarin nan gaba.

An dai yi jana’izar marigayi Abdulkarim da maraicen ranar Lahadi a makabartar Unguwar Sarki a garin Kaduna kamar yadda mataimaki na musamman ga mahaifin marigayin, Garba Mohammed, ya tabbatar.

XS
SM
MD
LG