Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya dai ta shirya gudanarda tarukan zaben shugabanninta a matakan kananan hukumomi a ranar Asabar hudu ga watan Satumba da mu ke ciki kafin umarnin kotun.
To sai dai a ranar Larabar da ta gabata ne wata babbar kotun tarayya a birnin Asaba na Jihar Delta ta ba da umarni na wucin gadi da ya dakatar da jam’iyyar ta APC daga shirya tarukan nata.
Amma kuma duk da hukuncin da kotun ta zartar har zuwa lokacin da za’a zartar da ainihin hukuncin kotun da ya hana ta gudanar da tarukan APC ta ce sai ta yi.
Haka kuma kotun ta ba da umarni ga shugabancin rikon kwarya na jam’iyyar APC karkashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe da sauran mambobin kwamitinsa da su daina gabatar da kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar.
Saidai shugaban riko na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana cewa umurnin kotu wanda ake zargin ya kore shi daga mukaminsa ba shi da wani tasiri a kansa.
Kalaman na gwamna Buni na kunshe ne a cikin wata sanarwar da daraktar yada labaransa, Mamman Mohammed, ya fitar a ranar Alhamis inda ya ce umurnin kotun ya takaita ne kan shugabancin jam’iyyar APC a jihar Delta ba shugabancin jam'iyyar na kasa ba.
A nasa bangare, sakataren riko na jam’iyyar APC, Sanata John James Akpanudoedehe, ya kaddamar da kwamitin da zai shirya taron a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, ya na mai cewa APC zata hukunta duk wanda ya kai ta kara gaban kotun.
A yayin kaddamar da kwamitin, Sanata Akpanudoedehe, ya umarci ,mambobin kwamitin su je su gudanar da aikinsu ba tare da wata fargaba ba.
Sanata Akpanudoedehe ya kuma jaddada matsayin kwamitin zartarwar Jam’iyyar ta APC a matakin kasa na cewa zata dauki hukunci mai tsauri a kan wadanda suka gurfanar da jam’iyyar a gaban kotu.
Yekini Nabena da ke zaman mataimakin sakataren yada labaran Jam’iyyar APC na kasa, ya bayyana cewa ba inda hukuncin babbar kotun da ke birnin Asaba na jihar Delta zai shafi ayyukan kwamitin APC.
Nabena ya kara da cewa jam’iyyarsa ta gudanar da tattaunawa mai zurfi da mambobinta sannan suka dauki matakin ci gaba da shirya taron na gobe Asabar kamar yadda suka amince a baya.
Idan ana iya tunawa, kotun ta birnin Asaba karkashin jagorancin mai shari’a Onome Marshal Umukoro, ta yanke hukuncin bayan zama da ta yi ne bisa karar da mataimakin shugaban jam’iyyar APC a jihar Delta, Olorogun Elvis Ayomanor, ya jagoranta da sahalewar wasu mambobin jam’iyyar da suka kalubalanci sakamakon babban taron zaben shugabannin jam’iyyar na ranar 31 ga Yulin da ta gabata.