Tun bayan sanar da matsayar cewa ya zama wajibi a maida ragamar mulki zuwa kudancin Najeriya da zarar shugaba Muhammadu Buhari ya kamamla wa’adin mulkinsa na biyu da gwamnonin yankin kudu su ka yi a karshen makon da ya gabata ne wasu ‘yan Najeriya ke fadin albarkacin bakinsu kan lamarin.
Wasu 'yan Najeriya sun bayyana cewa tsarin karba karba ba shi ne ya dace da tsarin mulkin Najeriya ba gara a samu dan takarar da zai yi wa mutane aiki ko daga wace kabila ya fito kawai kuma abi dimokradiyya a zabi dan takarar da ya fi cancanta.
Sai dai wasu na ganin cewa tun da ana cewa kasa daya ce tsarin karba karbar dai zai fi samar da zaman lafiya saboda kar wata kabila ta ga an hana ta an bai wa wata, wanda hakan zai iya kawo rashin zaman lafiya.
Kakakin kungiyar Dattawan Arewa wato NEF, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya ce su sun saba ganin irin wannan barazana ta dole a mayar da mulkin Najeriya kudu, wannan barazanar a zare wa ‘yan arewa ido a ce idan ba ku yi kaza ba za mu yi muku kaza sun dade su na ganinta a Arewa kuma basu tsoron ta.
Baba Ahmed ya kara da cewa duk wadannan abubuwan ba za su ba su tsoro ba kuma ba zai hana su su yi abin da suka san suna da yanci su yi ba, suna da yan ci kamar kowa amma kawai a ce su ja bakinsu su yi shiru mu zauna kawai mu yi layi mu je mu jefa wa dan kudu kuri’a.
Ya ce wannan ba zai yuwu ba saboda dimokaradiyya ake yi za su jefa wa wanda suka ga dama kuma suna kara tunawa 'yan arewa abin da suka san suna da shi a karkashin dokar kasa za su yi shi, idan ana son abu a wurin su abi su ta hanyar da za su iya yarda idan sun ga ba za a cuce su ba.
A wani bangare kuwa Sanata Rochas Okorocha mai wakiltar mazabar jihar Imo ta yamma a Majalisar Dattawa ya ce idan dai bahaushe ya ce ya kamata to yana nufin abin da ya kamata a yi ke nan, duk da ya ke ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya amma an sha yin haka na mulki ya koma kudu ko ya koma arewa kuma yanzu ace ba za a ci gaba da yin haka ba wannan bai da ce ba.
Okrocha ya ce ya fada wa mutanan kudu su daina fada a basu mulki hakan bai da ce ba amma ya kamata su rinka maganar da ta dace na cewa tun da arewa da yarabawa da kudu maso kudu sun yi mulki suma ya kamata a basu su dan taba a gani yadda za a samu kasar.
A baya-bayan nan dai an yi ta kiraye-kiraye kan batun yankin da ya kamata ya fitar da shugaban kasa na gaba idan shugaban Najeriya da ke kan karagar mulki Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa na shekaru 8 a shekarar 2023.
Idan ana iya tunawa dai, Najeriya ta koma tsarin mulkin dimokradiyya ne a shekarar 1999.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdul’rauf: