Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Sanata Ifeanyi Ararume A Matsayin Shugaban Hukumar Daraktocin NNPC


ABUJA: NNPC
ABUJA: NNPC

Bayan ba da umarnin yi wa kamfanin mai na Najeriya na NNPC rijista a matsayin kamfanin kasuwancia, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin shugabanni da za su jagorance shi.

A matsayinsa na ministan albarkatun man fetur, shugaba Buhari ya nada sanata Ifeanyi Ararume a matsayin shugaban daraktocin hukumar daraktocin kamfanin kasuwanci na NNPC.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina.

Shugaba Buhari ya ce matakin ya yi daidai da tanadin dokar man fetur na PIA, sashe na 53 sakin sashe na 1 na shekarar 2021.

Sashen dokar dai ya bukaci ministan albarkatun man fetur na kasar ya bayar da umarni a yi wa kamfanin kasuwancin NNPC rijista a cikin wata shida da fara aiwatar da dokar ta PIA, bayan tuntubar ministar kudi game da batun hannayen jarin kamfanin kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Idan ba’a manta ba, a watan Agustan shekarar 2021 ne shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan kudirin PIB zuwa dokar PIA, wadda ta yi tanadin sauya fasalin kamfanin NNPC ya koma kamfanin kasuwanci a maimakon hukuma ta gwamnati.

Shugaba Buhari (Twitter/ @BashirAhmaad)
Shugaba Buhari (Twitter/ @BashirAhmaad)

A cikin sanarwar, Adesina ya ce shugaba Buhari ya umarci shugaban kamfanin NNPC, Alh. Mele Kyari, ya dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da cewa an yi wa kamfanin na NNPC rijistar kamar yadda dokar PIA ta tanada.

Kazalika, Adeshina ya ce a bisa ikon da sashe na 59 sakin sashe na 2 na dokar PIA ya baiwa shugaba Buhari, ya amince da nadin hukumar daraktoci da hukumar gudanarwa ga kamafanin kasuwancin NNPC, wadanda za su fara aiki daga ranar da aka yi wa kamfanin rajista.

Sauran sabbin shugabanni hukumar daraktocin kamfanin NNPC din baya ga jagorar ta sanata Ifeanyi Ararume sun hada da dakta Tajudeen Umar daga Arewa Maso Gabas, Lami O. Ahmed daga Arewa ta tsakiya, Mallam Mohammed Lawal daga Arewa maso yamma, Sanata Margaret Chuba Okadigbo daga kudu maso gabas, da barista Constance Harry Marshal daga kudu maso kudu, sai kuma Cif Pius Akinyelure daga kudu maso yamma kamar yadda sanarwar ta bayyana.

A wani bangare kuma Mele Kolo Kyari shi zai ci gaba da zama a kan kujerar shugaban zartarwa na kamfanin, a yayin da Mal. Umar I. Ajiya zai zama babban jami’in kula da bangaren kudi na kamfanin.

Haka kuma, dokar ta PIA ta shekarar 2021 ta kuma tanadi ware wani kaso daga kudin shigar da ake samu na man fetur don raya al’ummomin yankin Naija Delta da ke samar da mai baya ga sayar da hannayen jarin kamfanin kasuwancin NNPC.

Gwamnatin Najeriya dai za ta tsame hannunta daga gudanar da harkokin kamfanin kasuwancin NNPC da zarar an kamalla aikin yin rajistar kamfanin.

Idan ana iya tunawa, jim kadan bayan zartar da kudirin PIB zuwa dokar PIA ne wasu mutanen yankin Neja Delta suka yi fatali da dokar, inda su ke korafi a kan kaso 3 bisa 100 da aka ware don raya yankunansu da ake aikin hako mai a cikin su.

XS
SM
MD
LG