Rahotanni sun yi nuni da cewa akwai rahotannin mutane da dama na neman kudin kasashen waje a bankuna da bizar karya, alhali suna yin amfani da kudadden ne a kasuwannin canjin kudi na bayan fage da wata manufa ta daban.
Shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana hakan a yayin magana a cikin shirin ‘siyasa a yau’ na gidan talabijan na Channels a lokacin da ya ke amsa tambayoyi kan lafiyarsa bayan jiri da ya ji a yayin gabatar da jawabi a wani taro da ya gudana a fadar Aso rock.
Bawa ya yaba da shirin babban bankin kasar wato CBN na sa ido tare da kama masu neman dala da manufar komawa kasuwannin canjin bayan fage don cin kazamar riba sakamakon yadda gwamnati ta janye ba da dala ga 'yan canji kai tsaye kamar yadda ta saba a da.
A cikin makwannin baya-bayan nan ne babban bankin Najeriya wato CBN ya sanar da cewa zai hada gwiwa da hukumar EFCC wajen kama masu karbo dala daga bankunan da bizar bogi don sayarwa a kasuwannin canjin bayan fage saboda karancin dala da ake fuskanta.
Hukumar EFCC dai ta yi marhabin da matakin kafa kwamitin sa ido da bankin CBN ya yi tare da hadin gwiwa da ita hukumar, don yaki da wadanda ke wannan dabi'a.
Kafin daukar matakin da CBN ya yi, Najeriya kadai ce kasa a duniya da ke baiwa yan canji kudadden waje daga lalitar babban bankin kasar wato CBN kai tsaye.
Bawa dai ya yi karin haske kan batun hana yan kasuwannin canji gudanar da kasuwancin su, ya na mai cewa babban bankin kasar dai ya daina ba yan canji kudi irin na waje kai tsaye ne kamar yadda aka saba yi a da tare da maida ba da kudadden ga bankunan kasar don rabawa wadanda ke amfani da su bisa tsarin kasuwanci, karatu ko neman ilimi da dai sauran su a maimakon baiwa yan BDC.
Haka kuma, Bawa ya ce hukumar EFCC na aiki da CBN, bankunan kasuwancin kasar da kwamitinsu, wajen samun bayanan sirri da ke taimakawa a aikin kama masu aikata irin wannan laifi ta hanyar neman kudadde da bisar bogi daga bankunan kasar don manufarsu kan samun kazamar riba da tsarin babban bankin kasar na taimaka mabukatan dala na kwarai.
Hukumar EFCC dai zata hukunta duk wadanda aka kama da aikata laifin amfani da bisar bogi wajen karbar dala daga bankunan kasar.
A game da yanayin lafiyarsa kuwa, Abdulrasheed Bawa, ya ce yana cikin koshin lafiya ya na mai cewa a yayin jawabi ya ji jiri ne, lamarin da ya sa shi neman gafarar mahalarta taron ya katse jawabinsa daga bisani ya je ganin likitarsa aka duba lafiyarsa aka gano bai da wata rashin lafiya, illa rashin ruwan jiki sakamakon kai komo kuma likita ya ba da shawarar ya yawaita shan ruwan.
Kazalika, Bawa ya yi karin haske game da shari’a tsakan EFCC da gwamnatin jihar kogi lamarin da ya sa aka rufe asusun gwamnatin jihar don gudanar da bincike, ya na mai cewa da zarar an kamalla binciken, EFCC za ta sanar da 'yan Najeriya sakamakon da aka samu.
Bawa ya mika godiyarsa ga miliyoyin yan Najeriya da su ka yi ta masa addu’o’i bayan bayyanar faifan bidiyo da ke yaduwa a kan ya sume a yayin gabatar da jawabi, in ji shi yana cikin koshin lafiya.