Hukumar SEC ta bayyana hakan ne a wata takardar da ta mikawa kwamitin hadin gwiwar majalisun Najeriya kan kudi, tsare-tsaren kasa, bangaren hakowa da sayar da man fetur, a karkashin jagorancin Sanata Adeola Solomon Olamilekan.
Kwamitin majalisar dattawa dai ya nuna damuwar cewa gibin da aka samu na iya sa a rufe hukumar ta SEC.
Babban daraktan hukumar SEC, Lamido Yuguda, ya danganta gibin da aka samu ga matsin tattalin arzikin da aka fuskanta a duk duniya sakamakon annobar korona birus, a wani zaman tattaunawa tare da mambobin kwamitin tsarin kudi na matsakaicin zango na shekarar 2022 zuwa 2024 wato MTEF da takardar kudi na FSP wato Fiscal Strategy Paper.
A cikin takardar da hukumar SEC ta mikawa kwamitin, hukumar ta bayyana cewa an sami gibin Naira biliyan 2.9 a shekarar 2019, Naira biliyan 4.3 a shekarar 2020 da da kuma Naira biliyan 1.7 ya zuwa watan Yuni na shekarar 2021.
Yuguda ya kara da bayyana cewa hukumarsa ta yi hasashen samun kudaden shiga da zasu kai naira biliyan 11.5 a shekarar 2021 sai kuma naira biliyan 11.2 a matsayin kudadden gudanarwata da biyan ma’aikata.
Da yake mayar da martani, Sanata Olamilekan ya bayyana cewa takardar da SEC ta mika ta yi nuni da cewa yanayin mara dadin ji ya bayyana cewa hukumar mai kula da hannayen jari da ba da izini ga kasuwancin da ke samun kudi ba ta samun kudin shiga.
Sanata Olamilekan ya kuma ce ya kamata hukumar SEC ta duba yanayin tsarin ma’aikatanta da kuma rage kudin da ake biya wajen ma’aikata don samar da kudadden shiga.
Kudadden gudanarwa hade da na biyan manyan ma’aikata na hukumar kadai na lakume kaso 70 cikin 100 na jumlar kudi Naira biliyan 9 kuma kaso 30 cikin 100 na kudadden kawai ke kai ga kananan ma’aikata.
Daya daga cikin mambobin kwamitin kudin dai, Sanata Kashim Shattima ya kalubalanci babban daraktar hukumar da ya yi nazari mai zurfi kan yadda hukumar zata habbaka aikin samun kudadden shiga.