Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Buhari Ta Ce Ta Yi Muhimman Ayukan Da Suka Gaggara, Wasu Sun Ce Basu Gani A Kasa Ba


Shugaba Buhari (Facebook/Min of Information)
Shugaba Buhari (Facebook/Min of Information)

Wasu 'yan Najeriya sun ce ba su gani a kasa ba, bayan Fadar shugaban kasar ta bayyana cewa shugaba Buhari ya bullo da manufofi, dokoki, da gudanar da muhimman ayyukan da kuma kammala wasu tun lokacin da ya dare kan karagar mulki a shekarar 2015.

A cikin wata sanarwa, mai taimakawa shugaban Najeriya kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya sami nasarori da suka hada da sanya hannu kan wasu kudurori 15 zuwa dokoki, da kammala manyan ayuka 17 a fadin kasar da dai sauransu.

Femi Adesina ya lissafa dokar masana’antar man fetur a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan shugaban wacce shugaba Buhari ya rattaba wa hannu a shekarar 2021 bayan shafe kusan shekaru ashirin ana kai-komo a kai.

Sanarwar ta ce a cikin kwanan nan kuma kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPC, ya sanar da samun ribar sa ta farko a cikin shekaru 44 da kafuwa a karkashin jagoranci shugaba Buhari, wanda ke sanya ido ga ma'aikatar albarkatun man fetur ta kasar.

Kazalika Adesina ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta kaddamar da shirin tallafawa al’umma na zamani na farko a tarihin Najeriya, yana mai jaddada cewa a yau shirin tallafi na socia investment shine mafi girman shirin tallafawa jama'a a nahiyar Afirka kuma daya daga cikin mafi girma a duniya.

Sai kuma kuma tsarin maida kasafin kudin gwamnatin tarayya zuwa tsari na farawa daga watan Janairu zuwa Disamba, bayan sama da shekaru goma da aka daina bin tsarin.

Sauran nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu sun hada da dokar kudi ta shekarar 2019 da 2020 wanda ita ce karo na farko da aka hada kasafin kudin tarayya tare da kwazo da takamaiman dokokin sake fasali don aikin aiwatarwa kamar yadda Femi Adesina ya bayyana da dai sauransu.

To sai dai kuma duk da haka wasu yan Najeriya sun bayyana cewa basu ga ni a kasa ba duk da shelar kawo ci gaba da gwamnatin ta ke yi.

Haruna Sule mazaunin Sabon Wuse a jihar Neja ya ce yan Najeriya na kara shiga halin matsi ne ba kakkautawa daga gwamnati.

Shi ma AB Tola ya ambato matsalolin tsaro su ke ci gaba da damun al’umma, ya na mai kira ga gwamnati da ta sake zage damste wajen yaki da 'yan tada kayar baya, saboda tsaron rayuka da dukiyoyi ne ke kan gaba a zukatan al’ummar Arewa a halin yanzu.

XS
SM
MD
LG