Dage sauraron shari’ar Nnamdi Kanu na zuwa ne bayan tawagar lauyoyinsa sun gudanar da wani tattaki kan matakin da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka dauka na hana wasu daga cikin lauyoyinsa damar shiga cikin kotun.
Wani kwamitin bincike da kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya wato ASUU ta kafa a jami’ar fasahar Owerri ta jihar Imo, ya ce an bi tsarin da ya dace wajen bai wa dakta Isa Ali Pantami matsayin farfesa a fannin dabarun tsare yan kasa a yanar gizo.
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana cewa Najeriya za ta kwashe tsawon shekaru 120 kafin ta kai ga samun wadatattun likitocin da ake bukata a fannin kiwon lafiya, kuma sai idan likitocin sun ci gaba da zama a kasar ba tare da ficewa ba.
Hukumar zabe ta Najeriya mai zaman kanta wato INEC ta dakatar da aikin tattara sakamakon zaben jihar Anambra da aka fara gudanarwa a ranar asabar inda ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
Tawagar hadin gwiwa ta jami’an tsaro a jihar Ekiti ta sami nasarar kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a wurin karbar kudin fansa a wani dajin da ke tsakanin iyakar jihohin Ekiti da Kwara.
Rundunar ‘yan sandan birnin Abuja ta tabbatar da ceto mutane 6 ciki har da malamai biyu da aka sace daga jami’ar birnin tarayya Abuja da aka fi sani da UNIABUJA.
'Yan takara 13 a zaben gwamnan jihar Anambra da ke gabatowa sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Awka, babban birnin jihar.
Rundunar sojin Najeriya ta sami nasarar halaka sama da ‘yan ta’adda 30 bayan wani samame da dakarun hadin gwiwa wato OPHK suka kai a wata maboyan ‘yan ta’addar a jihar Borno da ke yankin arewa maso Gabas.
Gwamnan Nyesom Wike na jihar Ribas, ya bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta yi binicke kan wadanda suka kutsa kai cikin gidan mai shari’a Mary Odili.
Matasa a jihar filato sun yi tattaki zuwa majalisar dokokin jihar Filato domin nuna bacın ransu kan tsige matashi dan uwansu wato kakakin majalisar, Abok Ayuba Nuhu da 'yan majalisar suka yi.
Rahotanni daga jihar Taraba sun yi nuni da cewa wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne sun rasa rayukansu a wani fadan raba kudin fansa da suka yi a tsakaninsu.
Mazauanan garin Damboa na ci gaba da tserewa don neman mafaka a garuruwa makwabta sakamakon harin da wasu mahara da ake zargin mambobin kungiyar Boko Haram ne suka kai a garin da maraicen ranar Alhamis.
Hamdok, masanin tattalin arziki ne da ya taba aiki da Majalisar Dinkin Duniya. An zabe shi a matsayin Firai minista na wucin gadi a watan Agustan 2019.
Fitaccen malamin addinin Musulunci a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi gargadin cewa ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda ba zai haifar da da mai ido ba.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta fara yiwa tsohon shugaban majalisar dattawa, Anyim Pius Anyim tambayoyi a kan zargin almundahana da karkatar da dukiyar jama’a.
Kungiyar BudgIT ta bayyana cewa jihohin Najeriya 3 ne kadai daga cikin 36, za su iya biyan albashi bayan da gwamnatin tarayya ta cire Naira biliyan 172 daga asusun kananan hukumominsu.
Ministan Shari’a kuma antoni janar na tarayyar Najeriya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa rahoton kwamitin da ofishinsa ya kafa ya yi nuni da cewa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya yi ta harzuka magoya bayansa ta kafar rediyo Biafra.
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da cibiyar Amana Sanatorium mai kula da mutanen da suka yi tu’amali da miyagun kwayoyi a baya a jihar Kano.
Wasu gungun mutane dauke da makamai sun kai hari kan ofishin yan sanda da bama-baman man fetur a karamar hukumar Isiala Mbano ta jihar Imo da yammacin ranar Alhamis.
Rahotanni daga najeriya na nuni da cewa wasu mayaka da ake zargin masu mubaya’a ga tsagin kungiyar ISWAP da Ansaru ne ke da alhakin tarwatsa hanyar jirgin kasa data ratsa daga Abuja zuwa Kaduna.
Domin Kari