Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wike Ya Ba Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana Biyu Ta Binciki Wadanda Suka Kutsa Gidan Mai Shari’a Odili


Atiku Abubakar Da Neysom Wike A Fatakwal
Atiku Abubakar Da Neysom Wike A Fatakwal

Gwamnan Nyesom Wike na jihar Ribas, ya bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta yi binicke kan wadanda suka kutsa kai cikin gidan mai shari’a Mary Odili.

A ranar juma’a ne wasu da ake kyautata zaton jami’an tsaro ne suka kai samame a gidan mai shari'a Mary Odili, lamarin da gwamna Wike ya bukaci gwamnati da ke kan karagar mulki ta binciki wadanda suka aikata hakan tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

A yayin jawabi ga manema labarai a Abuja, Wike yace gwamnati da al’ummar jihar ta Ribas na daukar matakai don tabbatar da cewa an binciko tare da hukunta duk wanda ke da hannu a cikin kutsen a ranar Lahadin da ta gabata.

Gwamna Wike ya kara da cewa suna zargin akwai wasu da ke yunkurin kashe mai shari'a Mary Odili, da mijinta da da sauran iyalinsu kuma da mutanen sun sami nasarar aikata hakan ba abinda gwamnati za ta yi illa ta ce za ta binciki lamarin kamar yadda ta saba cewa idan aka hallaka mutane.

Haka kuma, Wike ya ce lamarin bai da alaka da ministan shari'a na tarayyar Najeriya kuma ya ji dadin da shi ministan Malami ya fito ya ce ba shi da masaniya kan kutsen da aka kai gidan mai shari’a Odili.

A kan haka ya ce kasancewar gwamnati ba ta da masaniya kan lamarin ne ya sa al'ummar jihar suka ba da wa’adin sa’o’i 48 don bincikowa tare da bayyana musu wanda ke da alhakin kai samamen.

A cewar Wike, sa'o'i 48 sun isa ga kowace gwamnati ta bankado wadanda ke da hannu wajen mamaye gidan mai shari’a Mary Odili, ya na mai cewa idan wani abu ya faru da iyalin Dakta Peter Odili, to a tambayi gwamnatin Najeriya.

Tuni dai yan kasar ke ta bayyana mabanbantan ra’ayoyinsu a game da samamen da aka kai gidan Odili.

Jim kadan bayan samun labarin kai samame gidan mai shari’a Odili, ministan shari’a kuma antoni janar na tarayyar Najeriya Abubakar Malami ya nisanta kansa da samamen ya na mai cewa hakan ya saba doka.

A ranar juma’a ne mai taimakawa ministan shari’a kan harkokin yada labarai, Dakta Jibril Gwandu, ya musanta batun cewa minista na da hannu a cikin samamen da aka kai gidan Mary Odili a cikin sanarwar da ya fitar.

Dakta Jibril Gwandu ya ce tun da farko an sami kura-kurai a cikin takardun da aka shigar a gaban wata kotun majistare da ke Abuja don samun sammacin bincike wanda jami’an tsaron da suka mamaye gidan nata suka yi kokarin aiwatar da shi a gidan Mrs Odili a ranar Juma’a.

Kungiyar lauyoyin Najeriya wato NBA ta yi Allah wadi da sammen da aka kai gidan Mary Odili.

XS
SM
MD
LG